logo

HAUSA

Wasu Amurkawa na yunkurin kitsa labarai don bata sunan kasar Sin

2021-08-06 21:02:47 CRI

Wasu Amurkawa na yunkurin kitsa labarai don bata sunan kasar Sin_fororder_微信图片_20210806204858

Bisa umurnin da shugaban kasar Amurka ya baiwa hukumomin leken asirin kasarsa a watan Mayun bana, na gudanar da bincike kan asalin cutar COVID-19, nan da rabin wata, hukumomin za su gabatar da rahoton su na sakamakon binciken.

A halin yanzu, wasu Amurkawa ciki har da ‘yan jaridu, da ‘yan siyasa, da jami’an leken asiri da dama, suna yunkurin hada baki don kitsa labarai na shafawa kasar Sin bakin fenti.

Jiya ranar Alhamis, kafar yada labarai ta CNN ta ruwaito rahotanni dake cewa, wai hukumomin leken asirin Amurka sun samu wani muhimmin rumbun adana bayanai, dake kunshe da bayanan kwayar halittar gado, daga cibiyar nazarin kwayoyin cututtuka dake birnin Wuhan na kasar Sin, har ma an ce, idan aka yi nasarar tona asirin bayanan, za’a iya gano ainihin asalin kwayar cutar COVID-19. Amma rahotannin sun ce, ba’a san yaya, ko kuma yaushe hukumomin leken asirin Amurka suka samu bayanan ba.

Babu kwararan shaidu, sai dai jirkita gaskiya kawai, wato ainihin makasudin kafar CNN shi ne, karkata hankalin duniya kan cibiyar nazarin kwayoyin cututtuka dake birnin Wuhan, gami da bata sunan kasar Sin.

Baya ga hukumomin leken asiri gami da kafofin watsa labarai, akwai kuma wasu ‘yan siyasar Amurka wadanda su ma suke yunkurin shafawa kasar Sin bakin fenti.

Wasu Amurkawa na yunkurin kitsa labarai don bata sunan kasar Sin_fororder_微信图片_20210806204904

A halin yanzu, annobar COVID-19 na ci gaba da bazuwa a duk fadin duniya, musamman nau’ikan kwayar cutar da suke sauya yanayi. Ya zuwa ranar Alhamis, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a Amurka ya zarce miliyan 35, kana, yawan mace-macen ya zarce dubu 614, alkaluman da dukkansu ke kan gaba a duniya.

Abu mafi muhimmanci a halin yanzu shi ne, ceto al’umma da yaki da cutar. A jiya Alhamis kuma, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta yi kokarin samarwa duk duniya alluran riga-kafin cutar da yawansu ya kai biliyan 2, da bada kyautar dala miliyan 100 ga shirin COVAX, a wani kokari na yin raba daidan alluran riga-kafin ga kasashe masu tasowa. Wannan sabuwar gudummawa ce da kasar Sin ta bayar, ga hadin-gwiwar kasa da kasa a fannin yaki da cutar.

Kitsa labaran karya ba zai taimaka ga ceto Amurka, da duk duniya daga mawuyacin halin da suke ciki ba. Maimakon haka ya dace a girmama kimiyya, da zama tsintsiya madaurinki daya, don samun nasara kan wannan muhimmin yaki.  (Murtala Zhang)