Kamfanin hada motocin lantarki na Nijeriya na son hada gwiwa da takwarorinsa na kasar Sin
2021-08-06 13:07:37 CMG
Kamfanin Jet Motors dake hada motoci masu amfani da lantarki a Nijeriya, ya ce yana da burin zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin, domin lalubo damarmakin dake akwai a bangaren samar da motoci a Afrika da kuma kawo sauye-sauye ga bangaren a Nijeriya.
Bisa burin gaggauta samar da ci gaba a fannin ababen hawa a nahiyar Afrika ta hanyar samar da motocin lantarki masu rahusa, da kuma taimakawa wajen rage fitar da hayaki mai guba a titunan Afrika, kamfanin ya ce yana son cimma muradunsa, ta hanyar samun taimakon kwararru daga kasar Sin da sauran abokan hulda na kasashen ketare.
A cewar kamfanin, yayin da damar samar da motocin lantarki a Nijeriya ke kara fadada, shugaban kasar na kira da a zuba jari a bangaren makamashi mai tsafta.
Bisa la’akari da yadda man fetur ke gurbata yanayi da muhalli, motocin lantarki za su kai nahiyar Afrika ga cika alkawarin da ta yi karkashin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, na rage fitar da kaso 32 na hayaki mai guba ya zuwa shekarar 2030.
Ita ma gwamnatin Nijeriya, ta yi alkawarin rage fitar da hayaki mai guba da kaso 20, karkashin waccan yarjejejniya ta Paris. (Fa’iza Mustapha)