logo

HAUSA

Sharhi:Faduwa ta zo daidai da zama

2021-08-06 21:42:03 CRI

Sharhi:Faduwa ta zo daidai da zama_fororder_微信图片_20210806214008

Yanzu haka Nijeriya na fuskantar barazanar yaduwar cutar Covid-19 a zagaye na uku. Tun bayan da aka gano bullar cutar nau’in Delta karo na farko a kasar a watan da ya gabata, yawan masu harbuwa da cutar da wadanda cutar ta halaka sai karuwa suke yi cikin sauri. Alkaluman da cibiyar kandagarkin cututtuka ta Nijeriya ta fitar sun yi nuni da cewa, a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata, yawan sabbin masu harbuwa da cutar ya kai 590, wanda ya kai matsayin koli cikin watanni biyar da suka gabata.

Haka ma lamarin yake a sauran sassan Afirka, wadanda suke fuskantar saurin karuwar masu kamuwa da cutar da ma wadanda cutar ta halaka.

Mummunan yanayin cutar, ya kara tsananta matsalar karancin alluran rigakafin da kasashen Afirka ke fuskanta. Kwanan nan, hukumar lafiya ta Nijeriya a mataki na farko ta bayyana cewa, alluran rigakafi kimanin miliyan 4.02 da kasar ta karba daga shirin Covax sun kusan karewa. A ranar 2 ga wata kuma, kasar ta karbi karin wasu allurai miliyan 4.8. Duk da haka, me za su amfana wa kasar da ke da al’ummar da suka kai sama da miliyan 200? A sauran sassan Afirka ma, haka batun yake, inda aka yi wa mutane miliyan 21 kawai cikin baki dayan al’ummar nahiyar biliyan 1.3 riga kafin.

Yayin da kasashen Afirka ke matukar fama da karancin rigakafin, su kuma kasashe masu sukuni na yammacin duniya suna ta kokarin tara alluran fiye da bukatunsu, duba da cewa, galibin kasashen da suka yi wa sama da kaso 30% na al’ummarsu rigakafin, kasashen Turai da Amurka ne. Jaridar Washington Post ta wallafa wani sharhi a kwanan baya, inda take zargin Amurka da boye alluran rigakafi masu dimbin yawa. Sharhin ya ce, dalilin da ya sa Amurka ta tanadi allurai masu tarin yawa, shi ne sabo da tana son cimma burin da ta tsara a baya, na yiwa kaso 70 cikin 100 na baligan kasar alluran riga kafin a kalla daya kafin ranar 4 ga watan Yuli, wanda abu ne mai matukar wahala. Yanzu haka ma, akwai miliyoyin alluran da wa’adinsu ke kokarin karewa da Amurkar ta boye, kuma babu abin da za a yi da su sai dai a zubar da su a kwandon shara. Shi kuma strive masiyiwa, wakilin kungiyar tarayyar Afirka a bangaren sayen alluran rigakafi ya yi zargin cewa, “Ita kanta tarayyar Turai duk kanwar Ja ce, domin ba ta sayar wa kasashen Afirka rigakafi ko guda ba.”

Annobar Covid-19 babban kalubale ne da duniya baki daya ke fuskanta, kuma yadda za a kai ga raba rigakafi cikin adalci babban abu ne da ya kamata a daidaita a kokarin shawo kan annobar, musamman ma a taimaka wa kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa samun rigakafin da za su iya saya.

Faduwa ta zo daidai da zama, yadda aka kira taron dandalin hadin gwiwar samar da rigakafin Covid-19 na kasa da kasa a jiya da dare, taron da kasar Sin ta ba da shawarar shirya shi, wanda kuma ya gudana ta kafar bidiyo. A yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin rubataccen jawabi, inda ya ce, kasarsa za ta ci gaba da himmatuwa wajen taimakawa kasashe masu tasowa shawo kan yaduwar annobar, kuma a shekarar da muke ciki, za ta samarwa duk duniya alluran riga-kafin da yawan su ya kai biliyan 2, tare da samar da kyautar dala miliyan 100 ga shirin COVAX, a wani mataki na yin raba daidan alluran riga-kafin ga kasashe masu tasowa.

Kafin wannan, tuni kasar Sin ta samar da allurai sama da miliyan 750 ga kasashen ketare, matakin da ya sa ta zama kasar da ta fi samar da rigakafi a duniya. A watan da ya gabata kuma, gamayyar kungiyar dake samar da rigakafi ta duniya (GAVI) ta daddale yarjejeniyar sayen rigakafi daga kamfanin Sinopharm da na Sinovac na kasar Sin, hakan ya sa kamfanonin biyu suka fara samar da rigakafi ga shirin Covax. Ban da haka, kasar Sin ta raba fasahohinta tare kuma da aiwatar da hadin gwiwar samar da rigakafin da kasashe masu tasowa da dama, kawo yanzu, masana’antun harhada rigakafi na kasar Sin sun fara aikin samar da alluran rigakafi a kasashen Masar da Indonesia da Malaysia da Brazil da Turkiyya da Pakistan da Mexico da sauransu, kuma ana ganin yawan alluran da za su samar zai wuce miliyan 200.

A yayin da ake fuskantar annobar Covid-19, ba wanda zai iya samun cikakkiyar kariya har sai kowa da kowa ya samu kariya. Sanin kowa ne cewa, taimaka wa kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa wajen samun rigakafi cikin adalci, zai amfanawa duniya baki daya, sai dai kasashen yammacin duniya da kasar Sin, sun bambanta a matakan da suke dauka. Tun da farko, kasar Sin ta sanar da samar da rigakafin a matsayin kayan da zai amfanawa kowa a duniya, haka kuma ta yi ta kokarin samar da gudummawa ga kasashe masu tasowa. Sinawa kan ce, “zumunci yana tabbata ne a lokacin wahala”, lalle kasashe masu tasowa ma sun fahimci cewa, wace ce aminiyarsu.(Lubabatu)