Masu Ninkaya da daga nauyi na kasar Sin sun shiga gaba wajen samawa kasar su lambobin zinariya a gabar da ake ban kwana da Chusovitina
2021-08-05 13:55:03 CRI
A ranar Lahadi, kasar Sin ta lashe lambobin zinari 3, a gasar wasannin Olympics na birnin Tokyo dake gudana yanzu haka. Inda ‘yan wasan kasar masu ninkaya, da masu daga nauyi suka yiwa kasar bajimta, a gabar da kuma a gasar ta bana, ake ban kwana da kwararriyar ‘yar wasan alkafura Oksana Chusovitina, wadda ke yin ritaya daga Olympics bayan gasar nan ta Tokyo.
Dan wasan daga nauyi na Sin Li Fabin, ya yi rawar gani a gasar ta birnin Tokyo ta wannan karo, bayan da ya lashewa Sin lambar zinari ta biyu a gasar ajin maza masu nauyin kilogiram 61. Ya kuma kafa sabuwar bajimtar gasar Olympic, inda ya daga nauyin kilogiram 172, ya kuma tara jimillar makin daga nauyi har kilogiram 313.
Da fari dai Li ya ce ya gamu da matsi wajen daga nauyi, amma daga bisani ya ci gaba da samun nasara har zuwa karshen gasar. Ya ce yawanci idan ka yi dan shakkun abokan karawa, kafi samun saukin lashe gasa.
A nasa bangare, abokin wasan Li wato Chen Lijun, shi ma fuskanci kalubale da fari, kafin daga bisani ya yi nasarar lashe lambar zinari ajin maza masu nauyin kilogiram 67.
Kaza lika kafin nasarar ta Li, ‘yar wasan ajin mata ta Sin Hou Zhihui, ta lashe gasar daga nauyi ta masu nauyin kilogiram 49 a ranar Asabar. Har ila yau, kamar yadda aka yi tsammani, ‘yan wasan ninkaya na kasar Sin Shi Tingmao da Wang Han, sun lashe lambar zinari a gasar ajin mata ta mita 3. Wadda ta zamo lambar zinari ta 5 da tawagar kasar Sin ta lashe a jere, tun daga lokacin gasar birnin Athens ta shekarar 2004. Kuma lambar zinari ta 3 da Shi ta lashe a gasar Olympic. Jim kadan bayan samun nasarar, Shi mai shekaru 30 ta bayyana cewa, nasara ba ta dogaro ga lambar zinari ko azurfa da aka samu, maimakon haka ta fi la’akari da hanyar da aka bi, domin yin nasara mai dadi ko maras dadi.
Ya zuwa ranar Lahadi, Sin ta lashe jimillar lambobin zinari 6. Inda ta shiga gaban kasashe dake takara a gasar. A kuma wannan gaba ne ake ban kwana da tauraruwar wasan alkafura da ta dade tana taka rawar gani a gasar, wato Oksana Chusovitina daga Uzbekistan, wadda a bana take cika shekaru 46 da haihuwa. ‘Yar wasan na ban kwana da gasar Olympics a bana, bayan da ya shiga gasar har karo 8. Duk da cewa a bana bata kai ga lashe lambar zinari ba
Lokacin da aka nuna sakamakon da ta samu, kasancewarta ta 11 a jerin masu fafatawa a bana, Chusovitina ta rika zubar da hawaye, yayin da alkalai, da masu aikin sa kai na gasar, da ma’aikatan watsa labarai, da sauran mahalarta gasar suka mike tsaye, domin jinjinawa wannan tauraruwa da ta sha halartar wannan gasa.
Bayan kammalar gasar, Chusovitina ta ce "Na jima ina shiryawa wannan gasa domin kammala wasa na a nan, amma abu ne mai wahala na iya yin cikakken shiri da zai wadatar. Na shafe tsawon lokaci ina wannan wasa, yanzu ba ni da lokaci mai yawa a wannan fage."
Ita ma kasar Japan, ta fara wasannin ta da kafar dama, inda ta samu lambobin zinari masu dama. ‘Yar wasan ninkayar kasar Yui Ohashi, ta lashe lambar zinari a ajin mata daidaikun ‘yan wasa na mita 400.
A gasar judo ma, ‘yan Japan Uta, da Hifumi Abe, sun zamo ‘yan uwan juna na farko na miji da mace, da suka yi nasarar lashe lambar zinari a wannan gasa ta Olympic a rana guda a tarihi. Uta ta yi nasara a gasar ajin mata masu nauyin kilogiram 52, yayin da yayanta Hufumi shi ma ya lashe lambar zinari kasa da sa’a guda da nasarar kanwarsa, a ajin maza masu nauyin kilogiram 66.
Kari kan hakan, dan wasan kasar Yuto Horigomen, ya zamo dan wasa na farko da ya lashe gasar wasan zamiya kan allon zamiya, ko “skateboarding” a gasar Olympics. Dan wasan mai shekaru 22 da haihuwa, ya fara da fuskantar kalubale a wasan, kafin daga bisani ya samu maki mafi yawa tsakanin abokan takararsa, inda ya kammala da jimillar maki 37.18.
Da yake tsokaci bayan nasarar da ya samu, Yuto Horigomen ya ce, "Lokacin da aka ayyana wasan zamayi na “skateboarding” a matsayin wasan da za a fara gudanarwa a gasar Olympic karon farko a hukumance, ban yi tunanin shiga ba. Amma daga bisani sai na fara shiri mai inganci, har zuwa matakin gasar ta Olympics da dukkanin kwazo na, kuma gaskiya na yi farin ciki sosai da na kai ga lashe lambar zinari a wannan karon".
A gasar wasan ninkaya, Ahmed Hafnaoui mai shekaru 18 a duniya daga kasar Tunisia, ya nuna bajimta, bayan da ya kammala gasar ajin maza ta mita 400 cikin mituna 3 da dakika 43.36, inda ya lashe lambar zinari ta wannan aji. Da wannan nasara, Ahmed ya kawo karshen babakeran da ‘yan wasan ninkaya na kasashen Australia, da New Zealand da wasu kasashen Asiya suka sha yi a wannan aji na gasa. Tun bayan shekarar 1992, ba wani dan wasa da ba dan yankin Asiya ko Oceania ba, da ya taba lashe lambar zinari ta wannan aji, sai a wannan karo da Ahmed Hafnaoui ya kafa sabon tarihi.
A bangaren ninkaya ta daidaikun ‘yan wasa ajin mata mita 400 kuwa, kasar Australia ta sake kafa sabon tarihi na lashe lambar zinari, bayan da ‘yar wasan kasar ta kammala ninkayar cikin mintuna 3 da dakika 29.69. Sai kuma dan wasar Amurka Chase Kalisz, wanda a gasar birnin Rio ta shekarar 2016 ya zo matsayi na biyu, a bana shi ne ya yi nasarar lashe lambar zinari a gasar ninkaya ajin maza ta daidaikun ‘yan wasa ta mita 400.
Har ila yau, dan wasan Amurka William Shaner, ya lashe lambar zinari ta gasar harbin bindiga ajin maza ta mita 10 da jimillar maki 251.6, yayin da dan wasan kasar Sin mai shekaru 16 wato Sheng Lihao, ya lashe lambar azurfa ta wannan gasa, sai kuma abokin wasan sa Yang Haoran da ya lashe lambar tagulla.
A gasar kwallon volleyball ajin mata kuwa, kungiyar kasar Sin mai rike da kambin gasar, ta yi rashin nasara a hannu Turkiyya. Yayin gasar an sauya kyaftin din kungiyar Sin Zhu Ting har sau biyu, kuma har aka kammala maki 4 kacal ta ciwa tawagar, sakamakon rauni da ta ke da shi.
Da take tsokaci game da wasan, Cansu Ozbay ta kungiyar Turkiyya, wadda kuma ta taba buga wasa tare da Zhu a kungiyar VakifBank Sports Club dake Turkiyya, ta ce “A shirye muka zo domin kare kwallayen Zhu, a duk lokacin da ya bugo mana kwallo, kusan mun kare dukkanin kwallayen ta”.
A nata bangare kuwa, Zhang Changning dake matsayin wadda ke kan gaba wajen zura kwallo a raga, a wannan wasa a bangaren kasar Sin, cewa ta yi "Ba mu yi wasa yadda muka saba ba. Dukkanin mu mun yi nadama. Ina fatan za mu yi gyara, mu kuma yi wasa bisa kwarewa a wasan mu na gaba.