Masu halartar gasar wasannin Olympics ta Tokyo tare da rayuwarsu masu haske da ban al'ajabi
2021-08-05 13:58:04 CRI
'Yar wasan kwallon tebur mai shekaru 58 a duniya Ni Xialian tana buga wasan a gasar wasannin Olympics ta Tokyo
Cikin wadanda ke halartar gasar wasannin kwallon tebur a birnin Tokyo, akwai wata ‘yar wasa mai suna Ni Xialian, wadda ke da shekaru 58 a duniya. Kuma ita ce mafin yawan shekaru cikin ‘yan wasan masu fafatawa a gasar wasannin Olympics na wannan karo. Bana, karo na biyar ke nan take halartar gasar Olympics.
Ta gama gasarta baki daya, bayan da ta yi rashin nasara a hannun wata ‘yar wasan kwallon tebur ta kasar Koriya ta Kudu, wadda ke kasa da ita da shekaru 40.
Ni Xialian, ‘yar wasan kwallon tebur ce ta kasar Sin. A shekarar 1983, ta zama zakara a wasannin kwallon tebur ajin mata, da ma wasannin kwallon tebur mai hade da maza da mata, a gasar wasannin kwallon tebur ta kasa da kasa. Sa’an nan, a shekarar 1986, ta fita daga kungiyar wasannin kwallon tebur ta kasar Sin. Hakan ya sa ta kasa samun damar shiga gasar Olympics, domin an fara shigar da wasan cikin gasar Olympics ne a shekarar 1988.
Bayan ta yi ritaya, Ni Xialian ta fara wani aiki na nuna kwarewa a kasar Luxembourg. A shekarar 2000, wato lokacin da take da shekaru 37, a karo na farko, Ni Xialian ta halarci gasar wasannin Olympics a birnin Sydney. A wannan karo, ta shiga jerin wadanda ke kan gaba su 16 a wasan mutum daya-daya. Daga bisani kuma, ta halarci gasar wasannin Olympics ta birnin Beijing ta shekarar 2008, da gasar wasannin Olympics ta birnin London ta shekarar 2012, da kuma gasar wasannin Olympics ta Rio ta shekarar 2016.
Haka kuma, a shekarar 2019, wato lokacin da take da shekaru 56, Ni Xialian ta sami lambar yabo ta tagulla, a wasan kwallon tebur ta mutum daya-daya, a gasar wasannin motsa jiki ta Turai, inda ta sami izinin shiga gasar wasannin Olympics ta birnin Tokyo.
A ganinta, cimma nasarar gasa ko faduwa a gasa, ba abin mamaki ba ne ga ‘yan wasan motsa jiki, amma, irin jin dadi da ta samu a gasar ya sa ta gamsu. Shi ya sa, a lokacin da aka tambaye ta, ko za ta ci gaba da halartar gasar wasannin Olympics a karo mai zuwa? Ta amsa cewa, “Never Say Never”! Wato ba za a iya cewa a’a ba!
Natalia Partyka, ‘yar wasa mai halargar gasar wasannin Olympics ce da ke da hannu daya
Natalia Partyka, ‘yar wasan kwallon Ping Pang ta kasar Poland ce, wadda ba ta da hannu na dama tun daga lokacin da aka haife ta, kuma ita ce ‘yar wasa daya kacal da ta halarci gasar wasan kwallon Ping Pang ta wasannin Olympics, da kuma gasar ajin nakasassu.
An haife ta a shekarar 1989, kwarewarta kan wasan kwallon Ping Pang ta fi ta dukkan ‘yan wasan ajin nakasassu. Ta taba halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing, tare da gasar ajin nakasassu ta Beijing, wadda ta kasance ‘yar wasa ta farko da ta halarci gasar wasannin Olympics da kuma gasar ajin nakasassu.
Wannan ne karo na hudu da Natalia Partyka ta halarci gasar wasan kwallon Ping Pang ta wasannin Olympics, da kuma gasar ajin nakasassu. Koda yake ‘yar wasan nakasassu ce, amma ta shaida tunanin wasannin Olympics kamar mai cikakkiyar lafiya.
Hend Zaza, ‘yar wasan kwallon Ping Pang ce mafi kankantar shekaru daga kasar Syria mai fama da yake-yake
Hend Zaza, an haife ta a shekarar 2009 a kasar Syria, ita ce ‘yar wasa mafi kankantar shekaru a gasar wasannin Olympics tun bayan shekarar 1968. Zaza ita ce kuma mace daya tak a cikin tawagar ‘yan wasan kasar Syria dake halartar gasar wasannin Olympics ta Tokyo, kana ita ce ‘yar wasan kwallon Ping Pang ta farko da ta samu izinin shiga gasar wasannin Olympics a tarihin kasarta ta Syria.
A kasarta ta kasar Syria, ana fuskantar yake-yake. A cikin rayuwar rashin sanin makoma, wasan kwallon Ping Pang shi ne abin da ya sa Zaza farin ciki, da yin imani da samun kyakkyawar makoma.
Bayan da Zaza ta zamo zakara a gasar wasan kwallon Ping Pang ta neman samun izinin shiga gasar wasannin Olympics ta Tokyo ta yankin yammacin Asiya a watan Febrairu na shekarar 2020, ta yi kukan farin ciki. Ta ce, wannan ce kyauta da na baiwa kasa ta Syria, da mahaifanta, da kuma dukkan abokai na.
A rana ta farko ta gasar wasannin Olympics ta Tokyo, Zaza mai shekaru 12 a duniya ta cimma burinta na halartar gasar wasannin Olympics, koda yake ba ta cimma nasara a wasan na farko ba, amma ta samu babban ci gaba kan rayuwarta, ta buga wasan kwallon Ping Pang.
Zaza ta ce, a cikin shekaru 5 da suka gabata, ta fuskanci kalubale da matsaloli daban daban, amma ta yi kokari don cimma burinta.
Oksana Chusovitina ‘yar wasan rawar motsa jiki da tsalle tsalle ta yi ban kwana da gasar Olympics
Oksana Chusovitina ‘yar wasan rawar motsa jiki da tsalle tsalle daga Uzbekistan, ta yi rawar gani a tarihin gasar Olympics, bayan da a bana ta kafa tarihin zuwa gasar har karo na 8.
Mai shekaru 46 da haihuwa, Oksana ta kammala gasar da ta shiga a birnin Tokyo a ranar Asabar din karshen makon jiya, inda masu kallo da alkalai, da sauran masu ruwa da tsaki suka jinjinawa kwazon ta.
Chusovitina, ta samu kaiwa har zuwa zangon karshe na wasan rawar motsa jiki da tsalle tsalle a gasar ta bana, inda ta shiga jerin ‘yan wasa 8 mafiya kwarewa. Duk da cewa makin da ta samu wato 14.166 bai kai ya ba ta damar kara wucewa gaba ba, zuwa wasan karshe na gasar.
Bayan kammala wasan na ta, mahalarta gasar dake cikin dakin wasan da take, sun tashi tsaye domin girmama Chusovitina, matakin da ya sanya ta zubar da hawaye yayin da take daga hannu da jinjina gare su.
Daga bisani Oksana ta shaidawa manema labarai cewa "Na ji dadi sosai. Na yi kukan murna, saboda goyon baya da na samu daga mutane masu yawa cikin tsawon lokaci. Ban damu da sakamakon ba, na yi farin ciki. Ina ban kwana da wasanni, yanayi ne mai faranta dai da kuma sanya damuwa."
A tsawon gasannin da ta halarta, Chusovitina ta lashe lambobin yabo 11, tana kuma iya nuna nau’oin fasahohi 5, wanda hakan ya sa aka sanya sunan ta cikin taurarin wasannin motsa jiki na tsalle tsalle na duniya na shekarar 2017.
An haifi Oksana a birnin Koln, na kasar Jamus, ta kuma fara shiga gasannin Olympics a matsayin mambar hadaddiyar tawagar ‘yan wasan kasar ta shekarar 1992, tun kafin a haifi kusan duk ‘yan wasan dake fafatawa a gasar Olympics ta Tokyo.
A gasar ta 1992, ta yi nasarar lashe lambar zinari a dukkanin fannonin gasar da ta shiga, daga nan kuma ta ci gaba da halartar dukkanin gasannin Olympic da suka biyo baya, inda ta wakilci tarayyar Sobiyet, da Jamus, da kuma kasar Uzbekistan.
Anna Kiesenhofer ‘yar Austria ta bayar da mamaki
Anna Kiesenhofer ta girgiza tunanin masu bibiyar gasar Olympics ta bana, inda ta lashe lambar zinari da tseren keke ajin mata ta daidaikun ‘yan wasa, a gasar birnin Tokyo da ke gudana yanzu haka.
Kiesenhofer, wadda tun daga shekarar 2017 zuwa yanzu, ba ta kulla wata kwangilar wasa da wani fanni na kwararru ba, ta shige gaba tun farkon tseren keke na kilomita 137 na filin tsere na Fuji, ta kuma yiwa sauran ‘yan tseren zarra tun kafin a kai ga layin karshe, da kusan nisan kilomita 40.
Da yake ba bu wasu na’urori na isar da bayanai, sai dai kawai kananan rukunonin ‘yan wasan dake fafatawa, da yawa ba su lura da cewa Kiesenhofer ta yiwa sauran ‘yan wasan rata, da kusan sana da mintuna 5 ba, don haka Annemiek van Vleuten ta kai ga layin karshe, dakika 75 bayan Kiesenhofer ta kammala tseren, tana murnar lashe lambar zinari da ta samu.
‘Yar wasan tsaren keke daga Italiya wato Elisa Longo Borghini, ita ce ta zo na 3, yayin da Lizzie Deignan daga Birtaniya ta zo na 11.
Kiesenhofer mai shekaru 30 a duniya, ta karanci ilimin lissafi ne a jami’ar Cambridge, kafin ta samu digirin digirgir daga jami’ar Catalonia. An ce a baya bayan nan tana yin wani bincike kan tasirin zafi a jikin dan Adam, wanda mataki ne na gano yadda za a iya tunkarar gasar Olympics din dake gudana yanzu haka a Japan.
A lokacin gasar, Kiesenhofer ta yi gaba, ta bar saura a wani yanki na tudu mai tsayin mita 3,000, duk da kalubalen hakan ta samu kaiwa ga nasara.
Wannan nasara da ta samu ta baiwa Austria damar samun lambar zinari ta farko, tun bayan gasar Olympics ta lokacin zafi a shekarar 2004.
Duk da cewa lambar azurfa da Van Vleuten ta lashe ba ita ce cikar burin ta a wannan gasa ba, duk da haka, za ta yi farin ciki da samun lambar, duba da yadda ‘yar wasan mai shekaru 38 ta sha fama da karaya har 3 a kashin bayan ta, lokacin wani mummunan hadari da ya ritsa da ita a gasar Olympics ta birnin Rio da ta gabata shekaru 5 da suka wuce.