logo

HAUSA

Matsalar Koma Baya Ta Kawo Cikas Ga Farfadowar Tattalin Arzikin Yankin Afrika Dake Kudu Da Sahara

2021-08-05 13:44:02 CRI

BY CRI HAUSA

Karon farko yankin Afrika dake kudu da Sahara, ya fuskanci koma bayan tattalin arziki a cikin shekaru 10 da suka gabata, duk da farfadowar da aka samu a bana a matakai daban-daban. Wani manazarci na ganin cewa, an samu farfadowa a yankin ne, sakamakon farfadowar tattalin arzikin sauran wurare, da karuwar farashin muhimman kayayyaki da nasarar da aka cimma wajen dakile cutar COVID-19, duk da haka, tattalin arzikin yankin ba shi da inganci sosai, da har zai iya dogaro da sauran wurare matuka, abin da ya sa makomar samun bunkasuwa yake fuskantar hadarin koma baya da matsalar samun allurar cutar da hauhawar farashin kaya ke haifarwa.

IMF ta sabunta rahoton hasashen bunkasuwar tattalin arzikin duniya da ta gabatar a kwanan baya, inda ta yi hasashe cewa, saurin bunkasuwar yankin Afrika dake kudu da Sahara zai kai kashi 3.4%. A cewar IMF, matsalar barkewar cutar dake kara tsananta a wurin, za ta kara yin matsin lamba kan farfadowar tattalin arzikin yankin.

Bankin duniya ya ba da rahoton hasashen bunkasuwar tattalin arzikin duniya a farkon watan Yuni, inda ya yi hasashe cewa, saurin bunkasuwar yankin Afrika dake kudu da Sahara zai kai kashi 2.8% a bana, adadin da zai karu zuwa 3.3% kan na badi. WHO ta nuna cewa, Najeriya da Afrika ta kudu da Angola da sauransu, na samun farfadowa sannu a hankali. Ko da yake ana kyautata yanayin tattalin arziki, amma cutar ta kawo babban cikas ga aikin kiwon lafiya da ba da ilmi da zuba jari da kuma bunkasuwar tattalin arziki, abin bakin ciki shi ne, wasu kasashe na fuskantar hauhauwar farashin kaya mai tsanani.

Shugaban babban bankin Najeriya Godwin Emefiele, ya bayyana a kwanan baya cewa, alkaluma na nuna cewa, tattalin arzikin kasar na samun kyautatuwa, amma babu tabbaci kan makomar farfadowarsa, saboda yadda cutar ke kan ganiyyarta a duniya, a wani mataki kuma, hakan ya dogara da yadda ake gudanar da aikin kandagarkin cutar da manufofin kudade da ake dauka. Bankin ya yi hasashe cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar a bana zai karu da kashi 3.15%.

Godwin Emefiele ya kara da cewa, kamfanin man fetur ta kasar ya ba da gudummawa matuka ga kudin shigar gwamnatin, abin da ya bayyana ci gaban da kasar ke samu ta fuskar yiwa tsarin tattalin arzikinta kwaskwarima. A don haka ya yi kira ga gwamnati, da ta kara goyon bayan kamfanin, don rage bukatun shigo da man fetur daga ketare.

Shugaban babban bankin SARB Lesetja Kganyago ya nuna cewa, a cikin watanni uku na farkon bana, saurin bunkasuwar kasar ya fi yadda aka yi tsammani sauri, saboda yadda ake ganin saurin bunkasuwar sana’o’i da dama da cinikayyar shige da fice. Bankin ya yi hasashe cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar a bana zai kai kashi 4.2%.

A dangane da bunkasuwar da kasar za ta samu a tsakiyar wannan shekara kuwa, Lesetja Kganyago na ganin cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar ya dogara ne ga ci gaban tattalin arzikin duniya, ana sa ran bunkasuwar cinikayyar shige da fice za ta samu bunkasuwa cikin sauri, matakin da zai kara kudin shigar jama’a. A sa’i daya kuma, karancin makamashi da rashin tabbacin manufofi, zai haifar da hadarin samun koma baya.

Dr. Patrick Njoroge, shugaban babban bankin kasar Kenya ya bayyana a kwanan baya cewa, Kenya za ta ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kaya, saboda karuwar farashin abinci da makamashi da manufofin haraji da aka dauka a kwanan baya. A ganinsa, karuwar farashin kayayyakin da aka shigo daga waje da karancin isashen abinci, su ne dalilai na hauhawar farashin kaya. Amma, a cewarsa, za a iya magance wannan matsala bisa raguwar bukatu nan gaba.

Darektar sshen WHO dake Afrika Dr Matshidiso Moeti ta nuna cewa, Afrika na fama da barkewar kwayar cutar COVID-19 a zagaye na uku. Ko da yake yawan masu harbuwa da cutar ya ragu kadan, amma Afrika ba ta magance wannan matsala daga tushe ba. Ya zuwa yanzu, kaso 1.6 cikin 100 na al’ummar yankin kawai aka yi musu allurar. Ana bukatar a kalla allura miliyan 820 kafin karshen bana, don yiwa kashi 30% na al’ummar nahiyar allurar sau biyu. (Amina Xu)