logo

HAUSA

Wasu ‘yan siyasar Amurka na amfani da batun gano asalin COVID-19 a matsayin wani makami da ka iya lahanta duniya baki daya

2021-08-04 20:50:22 cri

Wasu ‘yan siyasar Amurka na amfani da batun gano asalin COVID-19 a matsayin wani makami da ka iya lahanta duniya baki daya_fororder_微信图片_20210804204829

A ranar Litinin din farkon makon nan, jagoran kwamitin dake lura da harkokin waje a majalissar wakilan Amurka Michael McCaul na jam’iyyar Republican, ya fitar da wani rahoto mai kunshe da zargin cewa, wai cutar numfashi ta COVID-19 ta bulla ne daga dakin gwajin halittu na birnin Wuhan, tun kafin watan Satumbar shekarar 2019.

To sai dai kuma, rahoton bai gabatar da wasu shaidu ko sahihan dalilai na kimiyya ba.

Kafin wannan rahoto ma dai, wasu Amurkawa da dama sun rika kokarin shafawa kasar Sin kashin kaji, ta hanyar danganta bullar cutar COVID-19 da dakin gwajin na Wuhan ta ko wane irin hali.

Masu fashin baki, na ganin ya dace a mayar da hankali ga binciken kimiyya wajen gano asalin wannan cuta, ba wai siyasantar da batun ba. Kuma tabbas matakan Amurka na mayar da wannan batu wani makamin siyasa, na iya jefa duniya cikin hadari.

A daya hannu kuma, matakan da Amurka ke dauka a yanzu, suna dakile himmar sassan kasa da kasa na gano asalin cutar, tare da taka birki ga ci gaban da ake samu a kimiyyance a fannin yaki da cutar, kuma hakan rashin kyautawa ne ga al’ummun duniya, ciki har da Amurkawa su kansu.

Kari kan hakan, wasu ‘yan siyasar Amurka na ci gaba da kokarin jinginawa Sin, da ma wasu kasashen Asiya alhakin bullar wannan annoba ta COVID-19, wanda hakan ke ingiza yanayi na nunawa al’ummu ‘yan asalin asiya kyama, a wasu kasashen yamma ciki har da Amurka, kuma hakan na kara fadada yanayin nuna wariyar launi, da kin jinin wasu al’ummu.

A ranar Litinin, sama da jam’iyyun siyasa da kungiyoyin al’ummu 300, da masana na sama da kasashe da yankunan duniya 100, sun mikawa sakatariyar hukumar lafiya ta duniya WHO wata sanarwar hadin gwiwa, suna masu kira ga WHOn da ta gudanar da binciken kasa da kasa, game da asalin kwayoyin cutar COVID-19 cikin adalci da daidaito. Kana sun bayyana matukar adawa da siyasantar da wannan aiki. Wanda hakan ya nuna cewa duniya na da ra’ayi guda, don gane da bukatar gudanar da binciken asalin wannan annoba bisa gaskiya.  (Saminu)