Siyasantar da batun COVID-19 babbar illa ce ga Duniya
2021-08-04 09:19:12 CRI
Masana da bangarori daban-daban na ci gaba da nuna damuwa, kan yadda wasu kasashe ke siyasantar da batun COVID-19. A baya-bayan nan kasashe mambobin hukumar lafiya ta duniya WHO, sun amince cewa, bai kamata a sanya siyasa cikin batun gano asalin kwayar cutar COVID-19 ba.
Babban daraktan shirin kiwon lafiya na gaggawa na WHO Mike Ryan, ya sha jadadda cewa, abu guda da kasashe mambobin hukumar ke maimaitawa shi ne, a daina siyasantar da ilimin kimiyya, amma, abin bakin ciki shi ne, yadda wasu ke kokarin siyasantar da batun.
Ya ce, WHO na tuntubar kasashe da dama, ciki har da kasar Sin, kan mataki na gaba da ya kamata a dauka dangane da binciken gano asalin kwayar cutar. Buga da kari, wani sakamakon binciken da masana na CGTN suka gudanar, ya nuna cewa, masu amfani da Intanet sama da 81,600 cikin harsuna daban-daban, da suka shiga shirin kuri’ar jin ra’ayin jama’a game da batun gano asalin COVID-19, kusan ra’ayinsu ya zo daya, inda suka nuna rashin amincewa da rashin gamsuwa kan matakin Amurka da masu goya mata baya, ta hanyar siyasantar da batun gano asalin cutar, da kara nuna bambanci da haifar da tashin hankali a kan ’yan asalin Asiya dake kasar bayan barkewar cutar.
Masu fashin baki na cewa, abu mafi muhimmanci yanzu shi ne hadin kan kasa da kasa don gano asalin cutar ba tare da bata lokaci ba, don kawo karshen wannan masifa da ta jefa daukacin Bil Adama cikin mawuyancin hali. Haka kuka kamata ya yi, wasu ’yan siyasa su rika sadaukar da muradu da moriyar Bil Adama don cimma burinsu na siyasa ba. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)