logo

HAUSA

Kowa Ya Debo Da Zafi Bakinsa

2021-08-04 16:08:14 CRI

Kowa Ya Debo Da Zafi Bakinsa_fororder_微信图片_20210804160632

Yanzu haka abin da ke wadari a kafofin watsa labarai da shafukan sada zumunta a duniya, shi ne yadda masana da bangarori daban-daban na al’umma ke ci gaba da nuna damuwa, kan yadda wasu kasashen yamma, musamman Amurka da ’yan barandanta ke siyasantar da batun COVID-19.

Su ma kasashe mambobin hukumar lafiya ta duniya, sun yi ittifakin cewa, bai dace a sanya siyasa cikin aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19 ba, yin haka, babbar illa ce ga duniya baki daya. Haka ma jam’iyyu da kungiyoyin al’umma sama da 300, da kasashe da yankuna fiye da 100, sun gabatar da wata sanarwar hadin gwiwa ga sakatariyar hukumar lafiya ta duniya, inda suka jaddada bukatar kasashen duniya su kara yin hadin gwiwa wajen yakar cutar.

Babban abin da ke damun duniya a halin yanzu shi ne, yadda wasu ’yan siyasar Amurka ke neman yin fatali da sakamakon binciken farko na cutar da tawagar masana na WHO da takwarorinsu na kasar Sin suka gudanar a birnin Wuhan na kasar Sin, inda suke neman a sake gudanar da irin wannan bincike karo na biyu a kasar ta Sin. Wannan a cewar masu fashin baki, rashin adalci ne, kuma hawan kawara ne ga tsari na kimiya.

Sanin kowa ne cewa, aikin gano asalin kwayar cutar COVID-19, nauyi ne da ya rataya a wuyan kasashen duniya, kana shawarar aikin gano cutar a karo na biyu da sakatariyar WHO ta gabatar, bai dace da kudirin da aka tsaida a babban taron hukumar ba, kana kasashe mambobin hukumar, ba su tattauna batun ba. Haka kuma shirin bai dace da sabon sakamakon nazarin aikin gano asalin kwayar cutar a duniya ba. A saboda haka, shirin ba zai taimaka ga hadin gwiwar binciken gano asalin kwayar a duniya ba. Wannan wani makirci ne na neman mayar da hannun agogo baya a kokarin da duniya ke yi na yakar cutar. Amma Kifi yana ganin ka mai jar koma.

Abu mafi muhimmanci yanzu shi ne, hadin kan kasa da kasa don gano asalin cutar ba tare da wata rufa-rufa ko son kai ba, don kawo karshen wannan masifa da ta jefa daukacin Bil Adama cikin mawuyancin hali. Bai kamata, wasu ’yan siyasa su rika sadaukar da muradu da moriyar Bil Adama don cimma burinsu na siyasa ba.  (Ibrahim Yaya)