logo

HAUSA

Gaskiya game da Shisshigin Amurka A cikin harkokin cikin gida na Sin kan batutuwan da suka shafi Hong Kong

2021-08-04 21:08:51 cri

Gaskiya game da Shisshigin Amurka A cikin harkokin cikin gida na Sin kan batutuwan da suka shafi Hong Kong_fororder_src=http___www.hkstv.tv_ueditor_php_upload_image_20210804_1628069130218629&refer=http___www.hkstv

Tun lokacin da sabuwar gwamnatin Amurka ta hau kan karagar mulki, ko kadan Amurka ba ta canza danyen aiki irin na gwamnatin da ta gabata ba. Ta kai hari kan kasar Sin kan batutuwan da suka shafi Hong Kong, kuma ta tattara wasu kasashen yamma don hada kai tare, wajen zargin kasar Sin, har ma da sanya wai “takunkumi” kan jami'an kasar.

Yau Laraba kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, ya bayar da wani sharhi mai taken “Su wa ye 'yan siyasar Amurka dake goyon bayan juna? Gaskiya Game Da Shisshigin Amurka a Cikin Harkokin Gidan Sin kan Batutuwa da suka shafi Hong Kong," inda aka lissafa hare-haren da Amurka ta kaiwa Sin ba tare da hujja ba, kan batutuwan da suka shafi Hong Kong, tun bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta hau karagar mulki, kuma an dawo da gaskiya ta hanyar bayyana gaskiyar lamarin.

Sharhin ya ce, a ranar 11 ga watan Maris, bayan da Majalisar Wakilan Jama'ar Kasar Sin ta yanke shawarar inganta tsarin gudanar da zabe na yankin musamman na Hong Kong, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar da sanarwa don kai farmaki da bata sunan kasar, kana ta hada kai da kungiyar G7 don bayar da sanarwa, da nufin zargin kudurin na kasar. Kana a ranar 17 ga watan Maris, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar da sanarwar sanya wai “takunkumi” kan jami'an kasar Sin 24, ciki har da mataimakan shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar 14.

Sharhin ya kuma nuna cewa, yadda za a tsara, da inganta tsarin gudanar da zabe na yankin Hong Kong harkokin cikin gida na kasar Sin ne, babu wata kasa daga waje da ke da ikon yin kalamai marasa kan gado game da hakan.

A hakika, ita kanta Amurka tana da karfafan dokoki na hana tsoma bakin kasashen ketare a zabukanta. Majalisar Wakilan Amurka ta zartar da wani kudiri kan gyaran dokokin zabe. To, ko me ya sa Amurka da kanta ta iya gyara dokokin zabe kamar yadda take bukata a kowane lokaci, amma take da sha’awar yin barna game da aikin gyaran dokoki na wani yanki na musamman na kasar Sin?

Sharhin ya bayyana cewa, Amurka ta yi tsammanin cewa, ta hanyar saka "takunkumi" za ta "raunata babban ikon cin gashin kai na Hong Kong", wanda bai yi daidai da gaskiya ba. Ingantaccen tsarin zabe na yankin Hong Kong yana aiwatar da manufar "masu kishin kasa su yi mulkin Hong Kong", da tsaron kasa, da tsaron tsarin mulkin yankin, wadanda duk sun fi samun tabbaci bisa na da. A sa’i daya kuma, ya nuna yadda mazauna Hong Kong ke shiga cikin harkokin siyasa da daidaituwa. Mutane da kungiyoyi daga fannoni daban daban a Hong Kong, sun kaddamar da jerin ayyuka kamar talla, da bayyanawa, da sa hannu a yankin baki daya, mazauna Hong Kong sama da miliyan 2.38 sun rattaba hannu don goyan bayan kudurin Majalisar Wakilan Jama'ar Ƙasa, na inganta tsarin zaben yankin.

Bisa binciken da yankin Hong Kong ya yi don sauraron ra'ayin jama'a, an nuna cewa, mazauna yankin kusan kashi 70% sun yi imanin cewa, inganta tsarin zaben ya karfafa gwiwar jama'ar Hong Kong, kan makomar yankin a nan gaba.

Sharhin ya kara da cewa, “Rikicin Gyara Dokar Masu Aikata Laifi da suka gudu” wanda aka tayar a watan Yunin shekarar 2019 ya lalata tattalin arziki, da zaman rayuwar jama’a a Hong Kong. A wannan shekarar, tattalin arzikin Hong Kong ya samu koma baya karo na farko a cikin shekaru goma da suka gabata.

An soma kaddamarwa, da kuma gudanar Dokar Tsaron Kasa ta Hong Kong a karshen watan Yuni na shekarar 2020, wanda ta bude sabon yanayi a Hong Kong daga hargitsi zuwa bin doka. A farkon kwata na wannan shekarar, GDPn yankin Hong Kong ya karu da kusan kashi 8% bisa na makamancin lokaci a bara. Rahoton da Asusun Ba Da Lamuni na Duniya ya bayar ya sake jaddada matsayin Hong Kong, na cibiyar hada-hadar kudi ta duniya. Kana “Rahoton Zuba Jari na Duniya na 2021” wanda Taron Majalisar Dinkin Duniya kan Ciniki da Ci gaba wato (UNCTAD) ya buga ya nuna cewa, har yanzu Hong Kong na kasancewa ta uku a duniya, wajen samun hannun jari kai tsaye a shekarar 2020.

Binciken da aka yi kwanan nan ya nuna cewa, mazauna yankin sama da kashi 80% da aka tuntuba, sun yi imanin cewa tsarin zamantakewa da halin tsaro sun inganta.

Baya ga haka, a zama na 46 na taron majalisar kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, kasashe sama da 70 sun fitar da sanarwa cikin hadin gwiwa, inda suka bukaci bangarorin da abin ya shafa da su daina tsoma baki cikin harkokin Hong Kong, da harkokin cikin gida na kasar Sin. Haka kuma akwai kasashe sama da 20 da ke goyon bayan matsayin kasar Sin, da matakan da ta dauka kan batutuwan da suka shafi Hong Kong, ta hanyar ba da jawabai da sauran hanyoyin.  (Mai fassara: Bilkisu)