logo

HAUSA

Shu’aibu Abubakar Babaji: Ina so in bada gudummawa ta ga harkar bunkasa layin dogo a Najeriya!

2021-08-03 14:55:25 CRI

Shu’aibu Abubakar Babaji: Ina so in bada gudummawa ta ga harkar bunkasa layin dogo a Najeriya!_fororder_微信图片_20210802200009

Shu’aibu Abubakar Babaji, wani dalibi ne dan asalin jihar Bauchin Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatu a jami’ar Central South dake birnin Changsha na lardin Hunan. Malam Shu’aibu, wanda ke nazarin ilimin da ya shafi shimfida layin dogo, ya ce akwai abubuwa da dama da ya kamata ya koya daga kasar Sin, ganin yadda ayyukan sufurin jiragen kasa na kasar Sin ke bunkasa cikin sauri a duk fadin duniya.

Malam Shu’aibu, wanda ya samu tallafin karo ilimi daga shahararren kamfanin gine-gine na kasar Sin dake Najeriya mai suna CCECC, har ya fara karatu a nan daga shekara ta 2018, ya kuma bayyana ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu tsakanin Najeriya da kasar Sin, har ya ce yana fatan bada gudummawarsa ga farfado da harkokin layin dogon Najeriya, wadanda suka lalace sakamakon wasu dalilai a shekarun baya. (Murtala Zhang)