Ya kamata WHO ta gaggauta bincike a Amurka bisa ra’ayin jama’a
2021-08-03 19:53:04 cri
Kwanan baya, cibiyar kwararru ta CGTN karkashin shugabancin babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ta fitar da tambayoyin binciken ra'ayoyin jama’a, ga masu amfani da yanar gizo na duniya baki daya a cikin yaruka shida na Majalisar Dinkin Duniya. Sakamakon ya nuna cewa, kaso 83.1% na masu amfani da intanet suna goyon bayan binciken asalin annobar COVID-19 a Amurka.
Daga matsar da lokacin gano wanda ya kamu da cutar na farko a kasar Amurka gaba, zuwa samun masu cutar numfashi da ba a san dalili ba bayan rufe dakin gwaje-gwaje na Fort Detrick, zuwa samun karin lamuran tsaro game da cutar a cikin dakin gwaje-gwaje na Jami'ar North Carolina System, yayin da lokaci ke wucewa, karin shakku game da yanayin annobar da Amurka ke ciki na kara fallasa.
Musamman, Amurka tana bukatar amsa tambaya daga duniya: Wato batun ya aka yi ta san cewa za a sami barkewar cutar a Wuhan wata guda kafin aukuwar hakan? Rahotanni na wasu kafofin watsa labarai, ciki har da jaridar “The Time of Israel”, sun ce tun a Nuwamban 2019, bangaren sojan Amurka ya raba bayanan sirri tare da Isra’ila da NATO, inda ta yi hasashen cewa cutar na gab da barkewa, har ma da bayanan da suka ambaci birnin Wuhan na kasar Sin.
Dangane da wannan, kafofin watsa labarai na Rasha suna ganin cewa, “Bayanan sirri daga bangaren sojan Amurka ya wuce gaban lokacin gano asalin cutar zuwa kusa da wani da'awa mai rikitarwa, wato tawagar wakilan sojojin Amurka ta kawo cutar a Wuhan ne, lokacin da ta halarci Wasannin Soja Na Duniya a tsakiyar Oktoban shekarar 2019.”
Hakan ne ra’ayoyin jama’a. ‘Yan siyasar Amurka su kan ce, mutane suna da 'yancin sanin gaskiya. Tun da haka ne, bisa manufar nuna gaskiya a bayyane, ana bukatar Amurka ta bude kofa ga duniya don a yi mata bincike. A matsayinta na kwararriyar hukuma a duniya a fannin kiwon lafiyar jama’a, ya kamata WHO ta saurari ra’ayoyin jama’a, ta binciki kasar Amurka da aka fi nuna shakku a kan ta cikin sauri, don ba jama’ar kasa da kasa damar gane gaskiya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)