logo

HAUSA

Cutar da ta kama kasar Amurka

2021-08-02 08:40:41 CMG

Cutar da ta kama kasar Amurka_fororder_20210802-sharhi-cutar Amurka-Bello

Idan wata kasa tana da karfin tattalin arziki da na kimiyya da fasaha da aikin soja, amma ba wani abun da take son gudanar da shi a duniya, ban da ta da rikici, da hana sauran kasashe samun ci gaba. To, ma iya cewa kwakwalwan wannan kasa ya kamu da cuta. Yau bari mu dan tattauna cutar da ta kama kasar Amurka.

A ganina kasar Amurka ta kamu da cutar “Son nuna fin karfi”, wadda ta kan nuna wasu alamu guda 3:

Na farko, son ta da rikici maimakon hadin gwiwa da saura.

Kasar Amurka tana nuna fin karfi da yin babakere a duniya ne bisa fifikon da ta samu a fannoni 3: Kimiyya da fasaha, aikin soja, da kuma matsayi mai muhimmanci da kudin kasar Dala ya samu. Idan wata kasa ta zama mai iya takara da ita a daya daga cikin wadannan fannoni 3, to, nan take kasar Amurka za ta dauki matakan matsawa kasar lamba. Misali, kasar Japan ta samu ci gaba sosai a fannin hada ingantattun na’urori a shekarun 1980, inda ta fara takara da kasar Amurka, lamarin da ya sanya kasar Amurka ta dauki matakan hada-hadar kudi da na ciniki, wadanda suka gurgunta tattalin arzikin kasar Japan, har ma ta fada cikin wani yanayi na tafiyar hawainiya na tsawon shekaru 30. Ban da wannan kuma, kasashen Turai sun gabatar da kudin Euro a shekarun 1990, wanda ya girgiza matsayin kudin Dala na Amurka. Ganin haka ya sa kasar Amurka ta da yakin Kosovo, lamarin da ya haddasa janyewar jari daga nahiyar Turai, da raguwar darajar kudin Euro cikin sauri. Zuwa yanzu, kasar Amurka ta fara kallon kasar Sin a matsayin abokiyar gaba dake takara da ita, don haka tana ta yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin, da kokarin shafawa kasar kashin kaza, tare da neman hana ta samun ci gaba a fannin kimiyya da fasaha.

Na biyu, neman mayar da matsalar cikin gida ta zama ta sauran kasashe.

Bari mu dauki aikin raba dukiya a matsayin misali, inda ake ganin karin gibin dake tsakanin masu kudi da marasa karfi cikin al’ummar kasar Amurka, musamman ma cikin shekaru 30 da suka wuce. A shekarar 2020, kashi 1% na Amurkawa mafi samun kudi sun mallaki dukiyoyin da darajarsu ta kai dalar Amurka triliyan 34.2, jimillar da ta ninka ta dukiyar fiye da rabin al’ummar kasar har sau 15. Wannan babban gibin da ake samu ya sa ake fama da matsalar tashin hankali, da aikace-aikacen nuna karfin tuwo. Sai dai, ganin haka bai sa kasar Amurka ta fara daidaita tsarin karbar haraji, da na raba dukiyoyi ba. Maimakon haka tana kokarin dora laifi ga sauran kasashe, musamman ma kasashen da suka fi samun rarar kudi yayin da suke ciniki da kasar Amurka. Inda kasar Amurka ta keta ka’idojin cinikin kasa da kasa, don daukar matakai na siyasa, da yakin ciniki, da tilastawa kasashen raba moriya ga kasar Amurka, ta yadda za ta samu sauki kan matsalolin da take fama da su a cikin gida.

Na uku, matsalar rashin hankali da ake samu cikin al’umma.

Yayin da kasar Amurka ke neman nuna fin karfi a fannin hulda da sauran kasashe, tana rungumar ra’ayin Darwin, wato rashin kulawa da mutane marasa karfi a gida. Saboda haka, ana ta samun karin gibi tsakanin masu kudi da marasa karfi na kasar, kana aikin ilimi na jama’a shi ma ya zama mai koma baya, ta yadda ra’ayi na kin ilimi, da matsalar rashin hankali suka gama gari a kasar. Da ma, wasu mutane masu ilimi sun taba yin amfani da kafofin watsa labaru wajen daidaita tunanin jama’ar kasar. Amma bayan da aka karkata ga shafukan sada zumunta wajen neman samun labaru, ra’ayoyi na kin ilimi da kyamar kimiya da fasaha sun fara zama masu farin jini sosai a kasar Amurka, kana wasu ‘yan siyasa su ma sun fara yin magunguna marasa hankali don neman samun goyon baya daga karin mutane, lamarin da ya tsananta rikicin da ake samu tsakanin jam’iyyun siyasa na kasar.

Yanzu haka, yaduwar cutar COVID-19 ta tsananta yanayin da kasar Amurka take ciki, inda aka fara ganin alamu na wadannan fannoni 3 sosai:

A wannan lokacin da muke ciki na fuskantar annobar COVID-19 wadda ke haifar da barazana ga daukacin bil Adama, kasar Amurka ba ta san mene ne abun da ya fi muhimmanci ba, kuma ba ta san muhimmancin yin hadin gwiwa ba, kawai tana neman yin fito-na-fito da kasar Sin. Ko za a kawar da annobar a karshe? Mutane nawa ne za su mutu sakamakon cutar? Wadannan tambayoyi, a ganin kasar Amurka, ba su da muhimmanci. Batun da ya fi muhimmanci bisa tunaninta shi ne kar a ba kasar Sin damar wuce kasar Amurka a fannin karfin kasa. Saboda haka, a lokacin da kasar Amurka take fama da karin matsaloli a gida, ita ma ta dauki karin matakai don matsin lamba ga kasar Sin.

Sa’an nan, zuwa wannan lokaci, an fi samun masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar Amurka, da wadanda suka rasa rayuka sakamakon cutar. Duk da haka kasar ba ta son daidaita kuskurenta, maimakon haka tana ta kokarin dora wa kasar Sin laifi. Inda ta dauki matakin siyasantar da batun binciken asalin kwayar cutar COVID-19, da matsawa hukumar lafiya ta duniya WHO lamba don neman sa baki cikin aikin binciken asalin cutar.

Ban da wannan kuma, akwai dimbin jita-jita da karairayi da ke yaduwa a kasar Amurka, misali irinsu “ yin allurar sinadarin kashe kwayoyin cuta zai warkar da masu kamu da cutar COVID-19” da “ tashoshin fasahar sadarwa ta 5G suna yada kwayoyin cuta”, da kuma “an fara samun kwayoyin cutar COVID-19 ne daga wani dakin gwajin kwayoyin halittu dake birnin Wuhan na kasar Sin” da dai sauransu. A sa’i daya kuma, wasu magungunan da kwararu masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Amurka suka fada sun zama marasa tasiri. Misali, kwararren masanin ilimin cututtuka masu yaduwa na kasar Amurka, Anthony Fauci, ya nanata har sau da dama, cewa “babu wata shaida da ta nuna kasancewar asalin cutar COVID-19 cikin wani dakin gwaji”. Amma duk da haka, gwamnatin kasar Amurka sam ba ta so ta yarda da maganar Fauci, maimakon haka tana ta nuna haushi ga kasar Sin tamkar wani mahaukacin kare.

Yanayin cutar “Son nuna fin karfi” da kasar Amurka ta kamu da ita ya riga ya zama mai tsanani sosai, ganin yadda kasar take samun karin gibin tsakanin al’umma, da yadda take ta da rikici da sauran kasashe, da yada karairayi, da neman dorawa sauran kasashe laifi, da daukar karin aikace-aikace marasa hankali. Sai mu jira har zuwa wani lokacin da ta daina samun wani fin karfi, mu duba me za ta yi a lokacin. (Bello Wang)

Bello