logo

HAUSA

Farfesa Fayyad: Kar a siyasantar da batun binciken asalin cutar COVID-19

2021-08-02 14:11:04 CMG

Farfesa Fayyad: Kar a siyasantar da batun binciken asalin cutar COVID-19_fororder_20210802-bayani-Masar-Bello.JPG

A kwanakin nan, wasu ‘yan siyasa na kasashen yammacin duniya na neman siyasantar da batun binciken asalin cutar COVID-19, inda suka rika fadan wasu maganganu marasa tushe don shafa wa kasar Sin kashin kaza. Dangane da wannan batu, mamban kwamitin siyasa na jam’iyyar NPUP ta kasar Masar, kana farfesa mai nazarin tattalin arziki da zaman al’umma, Mista Sherif Fayyad, ya ce neman shafawa wata kasa bakin fenti, ba zai taimakawa aikin ganin asalin cuta ba, kuma bai kamata ba a siyasantar da aikin binciken asalin COVID-19.

Farfesa Sherif Fayyad ya ce, wasu ‘yan siyasan kasashen yammacin duniya, musamman ma, kasar Amurka, na kokarin shafa wa kasar Sin kashin kaza, kan batun binciken asalin cutar COVID-19, don neman kare moriyar kasashensu. A ganin Fayyad, ko kafin bullar cutar COVID-19 ma, kasashen yamma sun saba fakewa da wasu batutuwa na shiyya-shiyya don sukar kasar Sin, da neman hana kasar samun ci gaba. Fayyad ya ce,

“Yadda suke siyasantar da batun ganin asalin cutar COVID-19, ya yi kama da yadda suka siyasantar da wasu batutuwan cikin gida da masu alaka da kabilu na kasar Sin. Saboda kawai, suna neman kare moriyar kansu. Idan sun ga yiwuwar samun riba, to, za su iya daukar duk wani mataki, har ma sun yi amfani da batun tsanantar yanayin annoba, maimakon ba da tallafin jin kai don sassanta yanayin da ake ciki. A ganina, kasar Amurka da wasu kasashe, suna kokarin yaudarar al’ummar duniya, inda suke neman dora wa kasar Sin laifin da ba ta taba aikatawa ba. Hakan tamkar wata kwayar cutar siyasa ce, saboda babu gaskiya a ciki, kana ba a taba tantance batun da matakan kimiyya da fasaha ba.”

Game da wajibcin aikin binciken asalin cuta, Mista Fayyad ya ce, aikin yana da muhimmanci, domin duk wata annobar da ta abku, ya kamata a yi kokarin gano asalinta, ta yadda za a dauki matakan da suka dace don hana yaduwarta. Sai dai yayin da ake gudanar da aikin, ya kamata a tabbatar da adalci da gaskiya, sa’an nan a gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban don tabbatar da cewa, za a gudanar da dukkan ayyuka a fili, ba tare da rufa-rufa ba. Farfesa Fayyad ya kara da cewa,

“Lokacin da dan Adam ke tinkarar annoba, dole ne a yi kokarin binciken asalinta, ta yadda za a samu damar ganin bayanta. Sai dai don ganin an gudanar da wannan aiki yadda ya kamata, akwai bukatar hadin kan bangarorin kasa da kasa, kana a gudanar da bincike bisa tushen sakamakon nazarin da aka samu a fannin kimiya da fasaha, ba tare da la’akari da batun siyasa da na tattalin arziki ba. Yunkurin yin amfani da aikin binciken asalin cuta a matsayin wani makami don sukar kasar Sin, ba zai yi nasara ba, domin jama’ar kasashe daban daban sun san abubuwan dake faruwa. Sun kuma fahimci cewa, kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya, suna kokarin siyasantar da batutuwa da yawa, don kare moriyarsu kawai.”

Farfesa Fayyad ya jaddada cewa, al’ummar duniya suna son samun adalci da daidaito yayin da ake kula da al’amuran duniyarmu, don haka ba za su yarda da yunkurin siyasantar da aikin binciken asalin cuta ba. Dangane da yadda hukumar lafiya ta duniya WHO take neman gudanar da mataki na biyu na aikin binciken asalin cutar COVID-19 a kasar Sin, Mista Fayyad ya nuna rashin jin dadinsa, inda ya ce, kasar Sin ta yi kokarin hadin gwiwa da sauran bangarorin kasa da kasa, da yin mu’amala a kai a kai tare da hukumar WHO, da ba da dimbin tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19 da sauran kayayyakin da ake bukata ga kasashe daban daban, duk wadannan abubuwa, sun nuna yadda kasar Sin take kokarin samar da gudunmowa ga aikin dakile cutar a duniya. A cewar Farfesa Fayyad,

“Kasar Sin har kullum tana neman ganin an karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban, da kokarin musayar ra’ayi da hukumar WHO, inda take ba da taimako sosai ga aikin kiwon lafiyar al’ummar duniya, musmman ma a fannin tinkarar annobar COVID-19, hakan ya nuna cewa kasar Sin tana girmama hukumar WHO, da aikin da take gudanarwa na hadin kan kasashe daban daban don dakile annoba. Kasar Sin kasa ce mai mutunci, wadda ke kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta. Kana yadda kasar Sin ta taimaki kasar Masar wajen hada alluran rigakafin COVID-19 ya haifar da moriya ga Masar, da sauran kasashen Afirka. A ganina, ba za a gano asalin cutar COVID-19 ta hanyar nuna shakku ba, ya kamata a dauki hakikanan matakai.”(Bello Wang)

Bello