Ba Zai Yiwu WHO Ta Zama Makamin Siyasar Amurka Ba
2021-08-02 21:38:26 cri
Yayin da yake ganawa da Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a ‘yan kwanakin da suka gabata, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, ya yi ikirarin cewa, Amurka tana goyon bayan WHO wajen gudanar da karin binciken gano asalin cutar COVID-19 a kasar Sin da sauran yankuna, kuma ya bayyana cewa, wai ya kamata kasashen duniya su hada kai kan wannan batu.
Wata babbar kasa dake boye ainihin halin cutar da take ciki, da siyasantar da batun, da kuma hana hadin kan kasa da kasa wajen yaki da cutar, a yanzu haka tana kira ga kasashen duniya da su hada kai tare? Kowa ya san mene ne nufinta. “Goyon baya” dake bakin Blinken a hakika mataki ne da yake son dauka, na murkushewa, da bata sunan kasar Sin bisa hujjar WHO.
Kamar yadda masu nazari suka nuna, Amurka tana kokarin sake gina tasirin ta a cikin hukumar WHO, kuma tana yunkurin jagorantar wasu muhimman batutuwa, da nufin sanya kasar Sin cikin wadanda ake zargi, da “kwararar kwayar cuta daga dakin gwaji”. Masana a fannin kimiyya na duniya sun yi Allah wadai da wannan makircin na siyasa.
Wilson Edwards, masanin ilimin halittu daga Bern, Switzerland, kwanan nan ya gabatar da wani sharhi dake cewa, masana a fannin kimiyya suna fatan dawowar Amurka a WHO, zai karfafa kokarin da ake na yakar cutar COVID-19, da ceto rayuka mafi yawa, “Amma, abin takaici, dawowar Washington cikin WHO, ta shigar da abubuwa masu nasaba da takarar siyasa bisa yankunan duniya, a wannan hukumar duniya dake gaba a fannin kimiyya”.
A halin yanzu, nau’ikan cutar Delta na bazuwa a duk duniya, hakan ya sa yanayin rigakafi da shawo kan cutar ke kara rikitarwa da tsananta. A matsayinta na kwararriyar jagora a duniya wajen yaki da cutar, WHO na bukatar yin biyayya ga ruhin kimiyya, kuma ta kaucewa ba da hanya sakamakon matsin lamba da aka yi mata a fannin siyasa.
Kasashen duniya ma ba za su kyale Amurka ta yi wani abin da bai dace ba. Ya kamata su hada kai tare don dakile yunkurinta na yin amfani da WHO don siyasantar da batun, ta yadda za a tabbatar da aikin yaki da annobar kan hanyar daidai, da kuma samo gaskiyar asalin cutar ta hanyar kimiyya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)