logo

HAUSA

Yunkurin Amurka na sa kaimi ga kasashe makwabtan Sin da su hana ci gaban Sin ba shi da amfani

2021-08-01 21:06:04 CRI

Yunkurin Amurka na sa kaimi ga kasashe makwabtan Sin da su hana ci gaban Sin ba shi da amfani_fororder_0801-4

A kwanakin baya, manyan jami’an kasar Amurka suka kammala ziyararsu a kasar Sin da kasashen dake makwabtaka da Sin. Mataimakiyar sakataren harkokin wajen kasar Amurka Wendy Sherman ta kai ziyara kasar Japan, da Koriya ta Kudu, da Mongoliya, da kuma kasar Sin, kuma sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya kai ziyara kasar Indiya, kana ministan tsaron kasar Amurka Lloyd Austin ya ziyarci kasashe 3 na kudu maso gabashin Asiya, wadannan manyan jami’an kasar Amurka sun ratsa tekun Pasifik zuwa yankin dake kewayen kasar Sin don aiwatar da wai manufofin tekun Indiya da tekun Pasifik, da nufin sa kaimi ga kasashe makwabtan Sin su hana ci gaban kasar.

Koda yake Sherman ta bayyana yayin ziyararta a kasar Sin cewa, kasar Amurka ba za ta hana bunkasuwar kasar Sin ba, amma ayyukan da Amurka ta yi sun shaida cewa, furucinta bai yi daidai da abin da ta yi ba.

Game da aikin da Amurka ta yi a kewayen kasar Sin, kasashen kudu maso gabashin Asiya sun san yunkurinta, ba za su goyi bayanta ba.

Ya kamata masu tsaida kuduri na kasar Amurka su yi bincike kan abubuwan da Sin take mayar da hankali kan su. Kana Amurka ta gyara ra’ayoyinta da manufofinta marasa dacewa kan kasar Sin, kada a dauki Sin a matsayin abokiyar gaba, haka zalika ta yi watsi da manufofinta na sa kaimi ga kasashe makwabtan Sin su hana bunkasuwar kasar. Kowa ya sani, kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ta dace da moriyar kasashen biyu da kuma begen kasa da kasa. (Zainab)