logo

HAUSA

Alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta samar sun isa kasashen Tanzania da Uganda

2021-08-01 17:13:53 CRI

Alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta samar sun isa kasashen Tanzania da Uganda

Alluran rigakafin cutar COVID-19 da gwamnatin Sin ta samar sun isa tsibirin Zanzibar dake kasar Tanzania da yammacin jiya Asabar.

Ministan harkokin cinikayya da bunkasa masana’antu na tsibirin Zanzibar Omar Said Shaaban, ya godewa gwamnatin kasar Sin a madadin gwamnatin tsibirin Zanzibar. Ya ce, alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta samar za su taimakawa tsibirin yaki da cutar, kana za su kara sada zumunta a tsakanin Sin da tsibirin.

Har ila yau a jiyan, alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta samar suka isa kasar Uganda. Ministar kiwon lafiya ta kasar Ruth Aceng, ta jinjinawa kasar Sin bisa goyon bayan da take ba kasashe masu tasowa wajen yaki da cutar COVID-19. Ta ce, alluran za su biya bukatun kasar Uganda na samar da su ga jama’a masu bukata. (Zainab)