Yunkurin Amurka na siyasantar da kwayar cuta yana kara tsananta yaduwarta
2021-07-31 16:42:38 CRI
A kwanan baya, hukumar lafiya ta duniya ta sanar da cewa, adadin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a Amurka cikin makon jiya, ya kai 500,332, adadin da ya karu da kaso 131.17 bisa dari, idan aka kwatanta da adadin karuwarsu makonni biyu da suka gabata. Kawo yanzu Amurka ta kasance kasa mafi yawan masu kamuwa da cutar a makon jiya a duniya, kuma kwatankwacin adadin masu kamuwa da cutar, da wadanda suka rasu sakamakon kamuwa da cutar a kasar, sun kai matsayin koli a duk fadin duniya.
A halin yanzu nau’in kwayar cutar na Delta yana bazuwa cikin sauri a duniya, bil adama kuma, na ci gaba da kokarin dakile kwayar cutar COVID-19, a don haka ya dace sassa daban daban na kasashen duniya su hada kai domin cimma burin kawo karshenta. Duk da cewa Amurka ta sanar da cewa tana jagorantar aikin dakile annobar a fadin duniya, matakin da ta dauka, yana kara tsananta yaduwar cutar.
Kamar yadda aka sani, takarar dake tsakanin jam’iyyu daban daban na Amurka tana haifar da tsaiko ga kokarin dakile annobar a kasar, kuma an lura cewa, tsarin siyasar kasar shi ne dalili.
To, ta yaya al’ummun Amurka za su nuna rashin jin dadinsu yayin da suka ga gwamnatin kasarsu ta gaza cimma burin hana yaduwar cutar? An ga yadda gwamnatin kasar Amurka ke ci gaba da dora laifi kan wasu kamar yadda tsohuwar gwamnatin kasar ta yi, har ma take tayar da hankali a sassa daban daban na duniya.
Amma ba zai yiyu yunkurin siyasa ya sarrafa kwayar cuta ba, a maimakon haka, zai haifar da tsaiko ga kokarin kandagarkin annobar da kasashen duniya suke yi, har ya jefa daukacin al’ummun kasa da kasa, ciki har da Amurkawa cikin mawuyacin hali.(Jamila)