logo

HAUSA

Shugaban Uganda ya ba sojoji umarnin sa ido kan binciken masu cutar COVID-19 a filin jirgin saman kasar

2021-07-31 16:30:26 CMG

Shugaban Uganda ya ba sojoji umarnin sa ido kan binciken masu cutar COVID-19 a filin jirgin saman kasar_fororder_0731-Uganda-Faeza

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, ya ba sojoji umarnin karbar ragamar binciken masu COVID-19 a filin jirgin saman kasa da kasa na Entebbe.

Cikin wani jawabi da ya gabatar ta gidan talabijin, shugaba Musevi ya ba sashen kula da ayyukan lafiya na rundunar sojin kasar, umarnin binciken matafiya masu shiga da fita a filin jirgin saman.

Ya kuma bukaci ma’aikatar lafiya da hukumar kula da shige da fice da sauran hukumomin gwamantin kasar, su tabbatar da bada hadin kai ga ka’idojin da aka gindaya na yaki da cutar, kamar na gwaji da kebe wadanda suka kamu.

Ya kuma sanar da sassauta matakan kulle na kwanaki 42 da aka sanya, biyo bayan raguwar adadin masu kamuwa da cutar a kasar. (Fa’iza Mustapha)

Faeza