logo

HAUSA

An gudanar da taron yayata bikin baje kolin cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afirka karo na 2 a Guangzhou

2021-07-30 19:59:46 CRI

An gudanar da taron yayata bikin baje kolin cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afirka karo na 2 a Guangzhou_fororder_中非-1

A jiya ne aka shirya taron yayata bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na biyu, da taron yayata yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka na gwaji a birnin Guangzhou.

Mataimakin gwamnan lardin Hunan He Baoxiang, da mataimakin gwamnan lardin Guangdong Zhang Xin, da jakadan kasar Rwanda dake kasar Sin James Kimonyo na daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai. Wakilan kasashen Angola, da Congo(Brazzaville), da Ghana, da Cote d’Ivoire, da Mali, da Senegal, da Uganda, da sauran kasashen Afirka dake birnin Guangzhou sun halarci taron.

An kuma sanya hannu kan yarjejeniyoyi guda 8 yayin taron, inda darajar ayyukan kwangiloli ta kai dalar Amurka miliyan 830.(Ibrahim)