logo

HAUSA

Gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba

2021-07-29 18:28:29 CRI

Gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba_fororder_hoto

A gabar da sabon jakadan Sin a Amurka Qin Gang ke kama aiki, wani abu da ya ja hankalin masu fashin baki shi ne yadda jakada Qin, ya sake nanata manufofin kasar Sin, game da alakar ta da Amurka, wadanda har kullum ba sa sauyawa.

A jumlace sabon jakadan ya kara haskakawa duniya cewa, dangantakar Sin da Amurka dake da tarihin tsawon fiye da rabin karni, tana da tasiri matuka ga sassan biyu, da ma duniya baki daya, kasancewar kyautatuwarta na ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da samar da daidaito a harkokin diflomasiyyar kasa da kasa.

A hannu guda kuma, burin Sin shi ne sassan kasa da kasa su zage damtse wajen tunkarar kalubalen dake addabar duniya cikin hadin gwiwa. Kuma akwai babban nauyi kan Sin da Amurka, na ba da muhimmiyar gudummawar tunkarar irin wadannan kalubale, kamar na sauyin yanayi, da yakar cutar numfashi ta COVID-19 da batun tsaron kasa da kasa, da inganta muhallin halittu da dai sauransu. A lokaci guda, ya zama wajibi sassan biyu su kawar da yin fito na fito da juna, muddin dai aka son cimma manyan nasarori a harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi.

Dama dai masharhanta sun sha bayyana bukatar da ake da ita, ta Sin da Amurka su kada karfi da karfe waje guda, don magance matsalolin da duniya ke ciki. A kuma wannan gaba, ana iya cewa kalaman sabon jakadan na Sin a Amurka, sun sake jaddada muhimmancin wadannan kiraye kiraye. Bahaushe dai kan ce “Yiwa wani yiwa kai”, don haka dukkanin wadannan shawarwari, da jaddada matsaya da bangaren Sin ke yi a yau da kullum na da ma’anar gaske, kuma ya ragewa bangaren Amurka ya yi nazari, tare da duba na tsanaki, domin gyara kurakurai, da rungumar akidun da za su yiwa ita kanta Amurkar amfani, da jama’ar ta, da kuma sauran sassan duniya baki daya. (Saminu Alhassan)