Ba zai yiyu Amurka ta dora laifin yaduwar annoba ga wasu ba
2021-07-29 19:58:57 CRI
A kwanakin baya ne mujallar cibiyar kimiyya ta kasar Amurka ta fitar da wani rahoto mai ban mamaki, inda aka bayyana cewa, alkaluman nazarin masanan kimiyyar Amurka sun nuna cewa, kila adadin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar ya riga ya kai miliyan 65, wato adadin da aka fitar yanzu ya kai kaso 40 bisa dari na ainihin adadin kawai, lamarin da ya sake tunatar da jama’ar kasa da kasa cewa, Amurka ta gaza shawo kan annobar a cikin gida, kuma cutar tana bazuwa cikin sauri a kasar, take kuma bazuwa a fadin duniya saboda Amurka ba ta dauki matakin dakile fitarta zuwa ketare ba, ana iya cewa, Amurka tana yada kwayar cuta a fadin duniya.
Idan aka waiwayi yanayin bazuwar cutar a Amurka, ana iya fahimtar cewa, an gano mutum na farko da ya harbu da cutar COVID-19 a kasar a shekarar 2019, amma gwamnatin Amurka ta boye lamarin kuma ta matsa lamba ga masanan kimiyya wadanda suka yi gargadi kan batun, saboda moriyar siyasa.
Yanzu haka ‘yan siyasar Amurka sun kauda kai kan moriyar al’ummun kasar, kuma ba su kula da tsaron rayukan al’ummun kasashen duniya ba, alkaluman da gwamnatin Amurka ta fitar sun nuna cewa, tun daga watan Afililun shekarar 2020, har zuwa watan Maris din shekarar bana, gaba daya adadin Amurkawa wadanda suka fita zuwa kasashen waje ta sama ko kasa ya kai miliyan 23.195.(Jamila)