Barawo ne ke kiran kama barawo yadda Amurka ke matsawa WHO kan batun gudanar da binciken gano asalin cutar Covid-19 karo na biyu a kasar Sin
2021-07-29 21:32:47 CRI
Barawo ne kan yi kiran kama barawo.
Kwanan nan, sakamakon matsin lambar da Amurka ta yi mata, hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta ce za ta gudanar da binciken gano asalin cutar Covid-19 karo na biyu a kasar Sin, musamman ma za ta mai da hankali a kan cibiyar nazarin cututtuka ta birnin Wuhan. Matakin da kuma ya samu rashin amincewa daga bangaren kasar Sin.
Kullum kasar Sin take bude kofarta kuma ba tare da rufa rufa ba a kan batun binciken gano asalin cutar, wadda ta gayyaci masanan hukumar WHO zuwa nan kasar har sau biyu, baya ga kuma rahoton binciken da sassan biyu suka fitar ya shaida cewa, abu ne da bai yiwu ba an samu bullar cutar daga dakin gwaji, wanda kuma ya samu amincewa daga masanan kimiyya na kasa da kasa. Sai dai abin bakin ciki shi ne, WHO ta ci gaba da mai da hankalinta a kan dakunan gwaji na kasar Sin a shirinta na gudanar da bincike a zagaye na biyu, ba tare da yin la’akari da sauran batutuwan da ya kamata ta mai da hankali a kai ba, ciki har da bullar cutar a sassan duniya daban daban kafin ta bulla a birnin Wuhan. Don haka, abu ne da ya dace kasar Sin ta ki amincewa da wannan shirin binciken da aka siyasantar da shi. A sa’i daya kuma, ya kamata mu tambaya, me ya sa Amurka ta yi ta hura wutar yin binciken gano asalin cutar a kasar Sin?
A game da tambayar, Mr.Tom Fowdy, marubucin kasar Burtaniya, wanda kuma manazarci ne kan harkokin gabashin Asiya, ya ba mu amsa a wani sharhin da ya wallafa a kwanan baya ta kafar shafin gidan talabijin RT, inda ya ce, tuni rahoton da masanan hukumar WHO suka fitar ya bayyana cewa, bai yiwu ba cutar ta bulla daga dakunan gwaji, amma nan da nan an nuna shakku ga rahoton, sabo da shi ba abu ne da kasar Amurka take son gani ba.
Kawo yanzu, kasar Amurka ta zo na farko ta fannonin yawan al’ummarta da suka harbu da cutar Covid-19 da ma yawan mamata a sanadin cutar. A ranar 27 ga wata, yawan sabbin masu harbuwa da cutar a kasar ya kai 85326. Jerome Adams, tsohon shugaban hukumar lafiya ta kasar ya bayyana cewa, Amurka ta sake fada cikin mawuyacin halin a fannin dakile cutar. To, tambaya ita ce, a matsayinta na kasar da ta ci gaba ta fannin harkokin kiwon lafiya, me ya sa Amurka ta gaza wajen shawo kan cutar?
Ta fannin gano asalin cutar kuma, har yanzu akwai shakku ta fannoni daban daban. Karin rahotanni na nuna cewa, cutar ta bulla a sassan duniya da dama a karshen watanni shida na shekarar 2019, ko a kasar Amurka, an gano bullar cutar a a kalla jihohi biyar kafin an ba da rahoton bullar cutar a karo na farko a kasar. Baya ga haka, a watan Agustan shekarar 2019, an rufe cibiyar nazarin kwayoyin halitta na Fort Detrick sabo da batun tsaro, kafin daga bisani an fara gano bullar nau’in cutar numfashi a sakamakon shan taba na zamani, har akwai wasu masu cutar da suka nuna alamun da ba su da bambanci sosai da na cutar Covid-19 ba. Kasar Sin ta riga ta gayyato masanan hukumar WHO zuwa Wuhan don su yi bincike, To, me zai hana Amurka ma ta bude kofarta ga masanan don su gudanar da bincike dangane da cibiyar Fort Detrick da ma cutar numfashi sakamakon shan taba na zamani?
Amma ina ne dalilin da ya sa Amurka ke kokarin shafa wa kasar Sin bakin fenti a kan annobar? Idan mun yi nazari, bai wuce ga neman dora laifinta a kan kasar, don ta karkata hankalin al’umma daga yadda ta ci tura wajen shawo kan cutar a gida da ma abubuwan da aka nuna shakku a kai game da bullar cutar a kasar.
A takaice dai, Amurka na fakewa da sunan bincike wajen dora laifinta kan kasar Sin. A yayin da kasa da kasa ke fuskantar barazanar annobar, yadda Amurka ke kokarin siyasantar da batun ba zai amfanawa wajen hadin gwiwar kasa da kasa wajen shawo kan cutar ba.
A sama da shekaru 100 da suka wuce, annobar influenza ta halaka mutane miliyoyi, annobar da ta samu asalinta ne daga kasar Amurka, wadda daga baya ta yadu har zuwa Turai da ma gabas mai nisa, sai dai daga karshe an yi mata sunan “Spanish Flu”.
Ga shi yanzu, Amurka na neman sake dora laifinta kan wata. (Lubabatu Lei)