logo

HAUSA

Makomar Duniya Na Dogaro Da Hadin Kan Kasa Da Kasa Wajen Tinkarar Sauyin Yanayi

2021-07-28 18:11:14 CRI

图片默认标题_fororder_06B9F37F-C4C5-4AD0-8DCF-130C3FA7D43C

Daga Amina Xu

Kwanan baya, yanayi mai tsanani ya bullo a wurare daban-daban a duniya, mamakon ruwan sama da aka sheka kamar da bakin kwarya a lardin Henan na kasar Sin, yanayi mai matukar zafi da ba taba ganin irinsa ba a arewa maso yammancin Amurka da kudu maso yammacin Canada, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da dari. A tsakiya da yammacin Turai kuma, an fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 200, fiye da dubu kuma sun bace. Wadannan alkaluma sun tsorata mutanen duniya sosai.

Babban sakataren kungiyar kula da yanayiduniya Petri Taras ya shedawa manema labarai cewa, “babu shakka, sauyin yanayi ya kara haifar da yanayi mai tsanani a duniya.

Abin farin ciki shi ne, kasashe da dama sun fahimci wajibcin samun bunkasuwa mai dorewa, da na tinkarar sauyin yanayi. Kasar Sin ta ba da gundumawa sosai a wannan fanni, a yayin aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar na 13, Sin ta gudanar da aikin saukaka kwararowar hamada da fadinsa ya kai hekta miliyan 10.978, yawan sabbin fadama da take da shi ya kai hekta dubu 202.6, yawan wutar lantarki da Sin ta samar dogaro da makamashi mai tsabta ya kai KWhtriliyan 2.2, yawan gandun dajida take da shi ya karu zuwa cubic mita triliyan 17.56, sai kuma yawan itatuwa da Sin ta dasa ya kai matsayin farko a duniya. Ban da wanann kuma, domin tinkarar sauyin yanayi, Sin ta yi alkawari cewa, yawan hayaki mai dumama yanayin duniyarmu da za ta fitar zai kai matsayin koli kafin shekarar 2030, sannan za ta yi kokarin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060. Amma, hannu daya ba ya daukar jinka, ana bukatar hadin kan kasa da kasa don tinkarar wannan barazana da duk duniya ke fuskanta. Abin farin ciki shi ne, wasu kasashe sun sauke nauyin dake wuyansu suna daukar matakan da suka dace, sai dai Amurka a matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya, yawan hayaki mai dumama yanayi da ta fitar ya kai matsayin koli a duniya, kuma ta ki yarda da rage fitar da hayaki mai dumama yanayi da kashi 26-28% bisa na shekarar 2005 kafin shekarar 2025. Bugu da kari, tsohon shugaban kasar Donald Trump ya yi watsi da manufofin kare yanayi kimani 70 tare da sanar da dakatar da zuba jari ga asusun kiyaye muhallin halittu, har gwamnatinsa ta ki cika alkawarin da gwamnatin Barack Obama ta yi na zubawa asusun jarin dala biliyan 2. Ban da wanann kuma, saboda matsayi mai maras kyau da Amurka ke dauka, shugabannin G20 ba su kai ga cimma matsaya daya ba a gun taronsu tun daga shekarar 2017. Shin ko Amurka ta cancanci sunan babbar kasa dake sauke nauyin dake wuyanta, bisa daukar wadannan matakai maras kyau dake kawo babbar illa ga yanayi da muhalli?

Saboda haka, ana ganin Amurka matsayin “mai keta matsaya daya da aka cimma” kuma “mai haifar da matsala” a duniya. Wadannan matakan da Amurka ke dauka dangane da yanayi ba jama’arta kadai za su yi wa illa ba, har ma da daukacin al’ummar duniya. 

Aikin ceto da Sin take gudanarwa a Henan, ya bayyana matsayin da ta dauka wato “sanya rayukan jama’a a gaban komai da hadin gwiwa don ceton mutane”, tunani ne mai nagarta. A ganina, ya kamata duniya ta sanya batun yanayi a gaban komai don samun bunkasuwa mai dorewa. Hadin kan kasa da kasa don tinkarar sauyin yanayi, hanya ce daya tilo da za a iya bi don magance matsalar da amfanawa jama’ar duniya.

Ina fatan karin kasashe za su hada kansu da kara tuntubar juna da daukar matakan da suka dace don kiyaye muhalli da tinkarar sauyin yanayi. Kuma ina fatan wasu ‘yan siyasa za su yi la’akari da rayuwar jama’a da makomar Bil Adama a maimakon cimma burin siyasa

Makomar duniya makomar Bil Adama ce, kuma makomar Bil Adama na dogaro da hadin kan kasa da kasa don tinkarar sauyin yanayi. (Amina Xu)