logo

HAUSA

Masu amfani da intanet a duniya sun nuna adawa da yadda ake siyasantar da aikin gano asalin cutar COVID-19

2021-07-28 19:54:53 CRI

Masu amfani da intanet a duniya sun nuna adawa da yadda ake siyasantar da aikin gano asalin cutar COVID-19_fororder_728

A cikin ‘yan kwanaki biyu da suka gabata, wani bincike da kafar watsa labaran kasar Sin ta gudanar kan masu amfani da Intanet a duniya, ya janyo hankalin jama’a matuka. An dai fara binciken ne a ranar 24 ga watan Yuli, agogon birnin Beijing, cikin harsuna Sinanci da Turanci, da Rashanci da Faransanci, da Spaniyanci da kuma Larabci. An kuma tsara tambayoyi guda uku ne. Daga cikinsu, akwai tambayar da aka yi kan “Kuna ganin an siyasantar da aikin gano asalin cutar COVID-19”, matsakaicin kaso 83 cikin 100 na masu amfani da Intanet, wadanda suka amsa wannan tambaya a shafin sada zamunta na Facebook, sun yarda da wannan tambaya, sai kaso 90 cikin 100 na masu amfani da shafin Tiwita, wadanda suka amsa tambayar cikin harshen Spaniyanci, da kaso 88 cikin 100 cikin harshen Faransanci, da kaso 83 cikin 100 na masu amfani da harshen Rashanci a shafin Intanet ne suka nuna amincewarsu bi da bi.

A hannu guda kuma, dangane da tambayar da aka yi cewa, “Kuna goyon bayan a gudanar da aikin binciken a kasashe da dama” daga cikin masu bbibiyar shafin na intanet da suka kada kuru’unsu, kaso 83 cikin 100 na masu amfani da shafin Tiwita sun nuna boyon bayansu, yayin da kaso 79 cikin 100 suka bayyana nasu goyon bayan a shafin Facebook.

Bugu da kari, game da batun “Aikin gaggawa na shawo kan cutar a duniya”, masu amfani da shafin Intanet din, sun mayar da hankali wajen bayar da shawarwari, kamar fadada hanyoyin samar da rigakafi, da bayar da jinya, da kuma killace yankunan da aka samu barkewar cutar.(Ibrahim)