logo

HAUSA

Kan Mage Ya Waye

2021-07-28 15:27:54 CRI

Kan Mage Ya Waye_fororder_hoto

Tun lokacin da kasar Sin ta sanar da duniya rahoton bullar cutar COVID-19 ba zato ba tsammani a birnin Wuhan, da ma irin matakan da take dauka wajen dakile ta, wasu kasashen yamma, musamman Amurka da ’yan korenta, ke sukar matakan yaki da annobar da kasar Sin ta dauka a wancan lokaci, wanda kuma daga karshe, su ne suka ba ta nasarar shawo kan cutar a cikin kasar.

Abin ka da mai hali, aka ce ba ya sauya wa, bayan da wata tawagar masana ta hukumar lafiya ta duniya, gami da takwararta ta kasar Sin suka kammala aikin binciken gano asalin cutar a birnin Wuhan, a karshe kuma WHOn ta fitar da sakamakon wannan bincike, amma kwatsam Amurka ta ce wai, ba ta gamsu da wannan sakamako da duniya ta yi na’am da shi. Abin tambaya a nan shi ne, shin yaushe ’yan siyasar Amurka suka zama masana kimiya? Wannan wani salo ne, na boye gazawar mahukuntan kasar ta dakile cutar dake ci gaba da halaka rayuwan jama’a a cikin kasar ta Amurka.

Sanin kowa ne cewa, batun COVID-19, batu ne da ya shafi kimiya, don haka, kamata ya yi a bar masana kimiya masu gaskiya, kwarewa da kuma adalci su gudanar da aikinsu ba tare da an tsoma musu baki, ko neman bata sunan wata kasa ba.

Rahotanni na cewa, yanzu haka, sakamakon shisshigin Amurka na ganin wai sai an sake gudanar da aikin binciken gano cutar a karo na biyu a kasar Sin, ya sa hukumar WHO take fuskantar matsin lamba mai yawa, inda a yanzu haka wasu ’yan siyasa ke da’awar kwarewa a fannin nazarin kwayoyin cututtuka.

Duniya ta san cewa, kasar Sin ta amsa kiran WHO na gudanar da wannan bincike a cikin kasarta, don haka, ya kamata ita ma Amurka ta ba da damar gudanar da irin wannan bincike, musamman a dakin gwajin nan na Fort Detrick, da ma ragowar dakunan bincikenta dake kasashen ketare, kamar yadda tawagar masana da suka ziyarci Wuhan, suka ziyarci dukkan wuraren da suka bukata a ba su dama a lokacin da suke aikin binciken. Wannan shi ne adalci

Masana da dama sun yi hasashen cewa, kwayar cutar COVID-19 ta bulla ne daga halittu, kuma kuskure ne a yi zargin cewa, ta bulla ne daga dakin gwaji na Wuhan. Kaza lika, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa a fannin nazarin kwayoyin cutar. Kana kafin bullar cutar a Sin, an gano wadanda suka kamu da cutar a wasu sassan duniya.

Masu fashin baki na nanata cewa, nuna yatsa ko neman bata sunan wata kasa, da ma siyasanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar, ba za su haifar da ’da mai ido ba. Yanzu fa kan Mage ya waye. (Ibrahim Yaya)