logo

HAUSA

Kamata ya yi WHO ta biya bukatun jama’ar duniya na yin bincike a dakin gwaji na Fort Detrick dake Amurka

2021-07-28 11:28:32 CRI

Kamata ya yi WHO ta biya bukatun jama’ar duniya na yin bincike a dakin gwaji na Fort Detrick dake Amurka_fororder_微信图片_20210728094836

Bayan WHO ta gabatar da shirinta na binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19 a zagaye na biyu bisa tunanin cewa akwai yiwuwar fitowar cutar daga dakin gwajin hallitu, al’ummar duniya na bukatar WHO da ta yi bincike a dakin gwaji na Fort Detrick na kasar Amurka.

Ya zuwa ran 27 ga watan Yuni da misali karfe 6 na yamma bisa agogon Beijing, yawan Sinawan da suka yi rajista a kan yanar gizo don neman WHO ta yi bincike kan dakin gwaji na Fort Detrick dake Amurka, ya kai miliyan 14. A kwanakin baya, dan jarida kuma mai nazarin tarihi na kasar Rasha Tsargrad ya wallafa wani bayani mai taken “ko Fort Detrick mai cike da sirri ka iya zama asalin kwayar cutar COVID-19?”, inda ya nuna cewa, gwamnatin Amurka na yunkurin dora laifi kan kasar Sin game da asalin kwayar cutar, amma kuma an fi amincewa da kasar Sin maimakon kasar Amurka kan wannan batu. Shahararren mashawarcin kasar Philippines, Harman Tiu Laurel ya yi kira ga WHO da ta yi cikakken bincike a dakin gwaji na Fort Detrick. Ya ce, Amurka tana yunkurin baza jita-jitar wai kwayar cutar ta samo asali daga dakin gwaji na Wuhan, amma ba ta fahimci barazanar da take da ita a cikin kasarta ba.

Daukacin al’ummar duniya na bukatar a yi bincike a dakin gwaji na Fort Detrick bisa cikakkun dalilai.

A watan Yulin shekarar 2019, bangaren sojin Amurka ya rufe Fort Detrick ba zato ba tsamani, a sa’i daya kuma wata cutar dake da alaka da sigarin lantarki ta barke a jihohi daban-daban na kasar, wadda alamunta suka yi kama da na COVID-19. An yi hasashen cewa, kwayoyin cutar sun fito ne daga dakin gwaji na Fort Detrick, saboda wannan wuri na adana munanan kwayoyin cuta irin wadanda rundunar sojin Japan ta 731 dake yunkurin neman mallakar kasar Sin a yakin duniya na biyu ta yi amfani da su, wadanda ke da babbar illa ga Bil Adama. Ban da wannan kuma, haduran dake shafar tsaron dakin sun auku sau da dama a tarihi.

Amma, gwamnatin Amurka ta ki gabatar da karin bayanai game da Fort Detrick bisa dalilai na tsaron kasa, duk da cewa ana neman a gudanar da bincike kansa. Ba shakka matakin da Amurka ke dauka ya kara shakkun da ake da shi kanta, tun da an iya yin bincike a dakin gwajin hallitu na Wuhan, me zai hana yin hakan a dakin gwaji na Fort Detrick? Cutar COVID-19 ta haifar da dimbin asara ga dukkan Bil Adama, don haka, idan ana son kaucewa sake barkewar cutar, dole ne a yi bincike a kasashe daban daban.

Ya zuwa yanzu, an kawo karshen aikin bincike a kasar Sin, kuma WHO ta gabatar da rahoto a karshen watan Maris cewa, babu yiwuwar fitowar kwayar cutar daga dakin gwaji na kasar Sin. To, idan WHO na ganin cewa akwai yiwuwar cutar ta samo asali ne daga dakin gwaji, tilas ne ta yi bincike kan Fort Detrick, wannan bukata ce ta kimiyya da kuma al’ummar duniya baki daya.

Amma, a matsayin wurin da ka iya zama asalin cutar, Amurka ta gudanar da bincike, inda ta siyasantar da batu na kimiyya tare da dora laifi kan kasar Sin.

Tun daga watan Mayun bana, gwamnati mai ci ta Amurka ta rika karawa batun asalin cutar gishiri tana neman shafawa kasar Sin bakin fenti da dora mata laifi a wannan fanni. Kuma tana yunkurin cimma wannan mumunan buri ta hanyar neman hukumar leken asirinta da ta fitar da rahoton neman asalin cutar cikin kwanaki 90 da baza jita-jita a duniya da tilastawa WHO ta bi umurninta da sauransu, abin da ya keta ka’idojin neman asalin cutar a duniya.

Duniya na bukatar gaskiya kuma tana matukar adawa da siyasantar da batun. Rahoton jin ra’ayin jama’a da CGTN ta yi a daren ranar 26 ga watan Yuli na bayyana cewa, yawan mutanen duniya da suka kada kuri’u a yanar gizo da ya kai kashi 80% na ganin cewa, an siyasantar da batun neman asalin cutar. Wasu sun bayyana cewa, dole ne WHO ta kawar da matsin lamba iri na siyasa da take fuskanta, kana suna ganin cewa batun neman gano asalin cutar ya zama manufar da Amurka ke dauka don dakatar da bunkasuwar kasar Sin. Wasu sun bayyana cewa, kafofin yada labarai na Amruka suna yunkurin baza jita-jita game da hakan, gwamnatin Amurkar kuma na neman kakabawa Sin takunkumi bisa dalilin neman gano asalin cutar.

Matakan siyasa da Amurka ke dauka ba su samu amincewa daga al’ummar duniya ba, a maimakon haka, mutanen duniya na matukar son fahimtar sirrin da Amurka take kokarin rufewa kan dakunan gwajin hallitunta fiye da 200 da ta kafa a sassan daban daban na duniya. Kasar Amurka dake kiran kanta “abin koyi a fannin kare hakkin Bil Adama” ta yi biris da bukatun jama’a da keta ka’idojin kimiyya da jefa lafiyar al’ummar duniya cikin hadari, don haka ba ta cancanci ta yi ikirarin kare demokuradiyya da hakkin Bil Adama da take yi ba.

Ba wata kasa da za ta iya yin watsi da bukatun jama’a a duniya. Daga kasashen gabas zuwa na yamma, yawancin al’umma na ganin cewa, dole ne a yi binciek kan dakin gwaji na Fort Detrick. Kuma kamata ya yi WHO ta biya bukatun al’ummar duniya ta yi wa dakin gwaji na Fort Detrick da sauran dakunan gwajin hallitu na Amurka fiye da 200 a duniya cikakken bincike don mutunta kimiyya da kuma samar da gaskiya. (Amina Xu)