logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta aiwatar da ayyukan da aka bayyana a cikin takardu biyu da Sin ta gabatar mata

2021-07-27 15:47:30 CRI

Ya kamata Amurka ta aiwatar da ayyukan da aka bayyana a cikin takardu biyu da Sin ta gabatar mata_fororder_0727-1

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya yi shawarwari tare da mataimakiyar sakataren harkokin wajen kasar Amurka Wendy Sherman a birnin Tianjin dake kasar Sin a jiya, hakan karin shawarwari ne a fannin harkokin diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka, tun bayan da aka yi ganawa da Anchorage a karshen watan Maris na bana. A yayin shawarwarin, Sin ta bayyana matsayinta da ka’idojinta kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Amurka, da gabatar da ayyuka hudu da ya kamata Amurka ta dakatar da yin su, da bayar da takardu biyu don kalubalantar Amurka, da ta sauya mummunan tunaninta, da manufofi masu hadarin gaske da take aiwatarwa kan kasar Sin.

Game da matsin lambar da Amurka take yiwa Sin kan batutuwan gano asalin kwayar cutar COVID-19, da batun yankin Taiwan, da Hong Kong, da jihar Xinjiang, da yankin kudancin teku na Sin da sauransu, Sin ta kara bayyana rashin jin dadi ga Amurka a gun shawarwarin, ta kuma bukaci Amurka da ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, da kawo illa ga moriyar Sin, da nuna kin amincewa ga Sin, da nuna fifikon tunani.

Kana Sin ta kalubalanci Amurka da sauya tunaninta mai tattare da kuskure. A cikin takardun biyu da Sin ta gabatar, Sin ta bukaci Amurka da ta sauya manufofinta masu hadarin gaske da take dauka kan kasar Sin, kana akwai wasu batutuwan da Sin ta fi maida hankali a kan su. Bukatun Sin yana da dacewa, wadanda suka dace da hanyar farfado da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Tarihi na shaida cewa, za a samu moriya idan aka raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, kuma za a gamu da illa idan aka nuna kiyayya da juna. Sin ta riga ta bayyana matsayinta kan raya dangantakar dake tsakaninta da Amurka. A mataki na gaba, ko gwamnatin Amurka tana iya aiwatar da ayyukan da aka bayyana a cikin takardun biyu da Sin ta bayar gare ta ko a’a. Tilas ne Amurka ta koyi saurara da girmamawa juna, yayin da take mu’amala da Sin, da kuma yin kokarin hadin gwiwa da juna. (Zainab)