logo

HAUSA

Dabara ta rage ga mai shiga rijiya

2021-07-27 19:10:03 CRI

Dabara ta rage ga mai shiga rijiya_fororder_微信图片_20210727190918

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna jiya Litinin da mataimakiyar ministan harkokin wajen Amurka, Wendy Sherman dake ziyara a kasar Sin, inda suka tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashensu da kuma sauran wasu batutuwa da dama.

A baya-bayan nan, dangantaka tsakanin kasashe biyu masu karfin tattalin arziki da tasiri, na ta daukar dumi, lamarin da ko shakka babu ba su kadai zai yi wa illa ba, har ma da sauran kasashen duniya dake kallonsu a matsayin abun koyi.

Bayan sabuwar gwamnatin Amurka ta kama aiki a farkon bana, an yi tsammanin cewa za ta fito da sabon salon shugabancin da ya bambanta da wadda ta gabaceta saboda irin kure-kuren da aka tafka, amma abun takaici shi ne yadda ta dora a kan wannan tafarki, ta kara zage damtse wajen matsin lamba da tsoma baki cikin harkokin da ba ta da hurumi.  

Yayin tattaunawar, Wang Yi ya bayyana matsayin kasar Sin na jajircewa wajen kare muradunta, haka kuma ya gabatar da wasu sharwarwari. A cewarsa, bai kamata Amurka ta kalubalanci tsarin mulkin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin da manufofinta ba. Haka ne, ya dace Amurka ta rike girmanta, ta kyale kasar Sin ta tafiyar da harkokinta bisa tsarin da ta zaba, domin dukkan abubuwa sun shaida cewa, tafarkin da ta zaba, shi ne mafi dacewa da ita da kuma ci gaban al’ummarta. Kana shi ne ya kai ta ga matsayin da taka na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Na biyu, bai kamata Amurka ta kawo cikas ga ci gaban kasar Sin ba. Samun ci gaban kasashen duniya, abu ne da zai kyautata tsari da walwalar duniya baki daya, yayin da koma baya, zai haifar da matsin da tashin hankali. Kana babu inda aka ce kasa daya tilo ce kadai ke da ’yancin samun ci gaba. Don haka, bai kamata Amurka ta rika yunkurin kawo cikas ga ci gaban kasar Sin ba. Sin na dogaro ne da karfinta da na al’ummarta wajen samun ci gaba. Ta kan nace ga bin hanyoyin da suka halatta, ba wai danniya ko babakere ko mulkin mallaka ba. Tsarinta na neman ci gaba, ya yi hannun riga da tsohuwar hanyar mulkin mallaka da manyan kasashe suka bi. Maimakon kokarin kawo cikas, kamata ya yi Amurka ta nace wajen inganta neman ci gaba bisa hanyoyin da suka dace, ko ma ta yi koyi da kasar Sin, da yin takara mai tsafta.  

Na uku, ya kamata Amurka ta daina keta ikon mulkin Sin. Kamata ya yi ta tuna cewa, kasar Sin kasa ce mai cikakken iko dake wakiltar kafatanin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. kuma amincewa da kasancewar Sin daya tak a duniya, shi ne tushen huldar kasar da kasashen waje, kuma wannan manufa ce da Amurkar ta amince da ita.

Dukkan wadannan sun nunawa Amurka matsayin kasar Sin, kuma dabara yanzu ya rage mata, ko ta zabi zaman lafiya ko fito na fito, kowanne ta zaba, kasar Sin a shirye take. (Faeza Mustapha)