logo

HAUSA

Sin ta mayar da martani game da kiraye-kirayen da ake yi na ganin an gudanar da bincike a Amurka da dakin gwaji na Fort Detrick

2021-07-26 19:04:10 CRI

Sin ta mayar da martani game da kiraye-kirayen da ake yi na ganin an gudanar da bincike a Amurka da dakin gwaji na Fort Detrick_fororder_fort detrick

A kwanakin nan ne, kafofin watsa labarai da masana daga kasashe da dama suka bayyana ra’ayoyinsu, inda suke zargin kasar Amurka da siyasantar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19. Suna masu bayyana cewa, kamata ya yi a gudanar da irin wannan aikin bincike a kasar Amurka da ma dakin gwajin nan na Port Detrict. Da yake amsa tambayoyin manema labarai Litinin din nan kan wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, tuni duniya ta riga ta gano yadda Amurka take siyasantar da aikin binciken gano asalin cutar.

Da ya karin haske game da kiran da dubban miliyoyin Sinawa suka yiwa hukumar lafiya ta duniya(WHO), kan ta gudanar da bincike a dakin gwaji na Port Detrick dake Amurka kuwa, Zhao Lijian kira ya yi ga Amurka, kan me ya sa har yanzu ta rufe kunnenta kan kiraye-kirayen da dubban miliyoyin Sinawa suka yi na neman adalci? (Ibrahim)