logo

HAUSA

Kokarin tinkarar ambaliyar ruwa ya nuna hadin kan Sinawa

2021-07-26 15:34:11 CMG

Kokarin tinkarar ambaliyar ruwa ya nuna hadin kan Sinawa_fororder_Henan

A makon da ya gabata, an sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya inda ya haifar da ambaliyar ruwa a lardin Henan na kasar Sin, inda iska mai dauke da dimbin ruwa ta tashi daga yankin tekun Pasific ta shiga cikin saman lardin dake tsakiyar Sin, tare da haddasa saukar ruwan sama, da yawansa ya kai na ruwan sama da a kan samu a lardin cikin shekaru. Mummunar ambaliyar ruwan da aka samu a lardin, zuwa yanzu ta haddasa mutuwar mutane 63, da bacewar wasu 5.

Bala’in mai ban tsoro ne, sai dai a sa’i daya ya nuna yadda Sinawa suke kokarin hadin kai da juna a yayin tinkarar bala’in. Bayan da shugaban kasar Xi Jinping ya ba da umarni kan yadda za a gudanar da aikin ceton jama’a, a birnin Zhengzhou, hedkwatar lardin Henan, an samu ‘yan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jami’ai fiye da dubu 400, da sojoji 5290, da ‘yan sanda dubu 30, da masu aikin sa kai dubu 164, da mutane masu ba da taimako 5556 daga sauran sassan kasar, wadanda suka fara aikin kai dauki ga jama’a nan take. Ko da yake, ambaliyar ruwan ta lalata kayayyakin masu alaka da samar da wutar lantarki, da na ruwa, da zirga-zirgar motoci, da aikin sadarwa, amma ma’aikata fiye da dubu 10 sun yi kokarin gyaran wadannan kayayyaki ba dare ba rana, ta yadda aka samu nasarar daidaita galibin kayayyakin cikin kwanaki kalilan. Ban da wannan kuma, an yi kokarin tabbatra da samar da isashen abinci da ake bukata a kasuwanni, kana likitoci da masu aikin hana yaduwar cututtuka su ma sun fara aiki nan take a cikin uguwanni daban daban.

Wasu hotuna, da rubutattun bayanai da aka watsa ta yanar gizo ta Internet sun kuma nuna yadda mutane suka yi kokarin taimakawa juna yayin da ake tinkarar bala’in. Na ga yadda sojoji suke amfani da wata babbar motar yaki wajen kwashe jama’a daga wurare masu hadari. Kana na ga yadda a cikin wani jirgin kasa dake gudu a karkashin kasa, mutane suke tsayawa a cikin ruwa domin jiran zuwan ma’aikatan da za su kai musu dauki. Ko da yake sun shafe wasu sa’o’i suna tsaye cikin ruwa, amma bayan an fara janye su daga cikin jirgin, sun yi tafiya cikin tsari. Inda suke taimakawa juna wajen tafiya, da baiwa tsoffi, da yara, da mata damar fita daga cikin jirgin kafin saura. Sa’an nan na ga yadda masu aikin sa kai suke gudu a cikin ruwan sama, suke jagorantar motoci don magance shigarsu cikin wuraren dake da ruwa mai matukar yawa. Duk lokacin da wani mutum ya fadi cikin ruwa, nan da nan wasu mutane za su je kusa da shi don taimakawa ceton shi daga cikin ruwan. Kana an yi amfani da kafofin da kamfanin CMG da sauran hokumomi suka samar, wajen watsa sakonnin neman taimako, ta yadda masu aikin ceto za su san inda ake bukatar taimako.

Ban da wannan kuma, kamfanonin kasar da yawa su ma sun yi kokarin ba da taimakonsu. A birnin Zhengzhou, otel-otel sun rage farashin dakunansu, don samar wa mutanen da ba sa iya komawa gidajensu. Wasunsu kuma sun shimfida kushin a kasa, da baiwa mutane darduma, domin su yi amfani da kayayyakin ba tare da biya kudi ba. Wasu manyan kamfanoni mallakar gwamnati sun ba da tallafin kudin da ya kai dala miliyan 150 ga lardin Henan. Wasu kamfanoni sun bude rumfunansu don samar wa jama’a da abinci, ba tare da karbar kudi ba. Kana wani abun ban sha’awa shi ne, wani kamfanin samar da tufafi da takalma, ko da yake bai ci riba ba a wadannan shekaru, amma duk da haka, ya ba da tallafin kayayyakin da darajarsu ta kai dala miliyan 7 da dubu 720, lamarin da ya burge mutanen kasar Sin sosai. Daga bisani, don nuna goyon baya ga wannan kamfani, wasu mutane fiye da miliyan 10 sun shiga shafin sayar da kaya na kamfanin, inda suka sayi kayayyaki masu dimbin yawa, har ma wasu nau’o’in kayayyaki sun kare nan take.

Ganin wadannan abubuwa, watakila za a yi mamakin yadda Sinawa suke kokarin hadin gwiwa da juna. Amma ina dalilin da ya sa Sinawa suke yin haka? To, dalilan sun shafi halayyar dan Adam na taimakawa juna, yayin da ake fuskantar matsala, da yadda ake samun wata jam’iyyar da take taimakawa kokarin jama’ar kasar Sin na hadin gwiwa a cikin al’umma, wato jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. A matsayinta na jam’iyya mai mulki a kasar, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta iya hada bangarori daban daban a waje guda, don samar da dauki ga jama’a cikin sauri. Ban da wannan kuma, jam’iyyar ta yi matukar kokari wajen gudanar da aikin ceto, saboda a birnin Zhengzhou kadai an samu ‘yan jam’iyyar da jami’an gwamnati 7, wadanda suka sadaukar da rayukansu, yayin da suke kokarin kai dauki ga jama’ar birnin.

A karshe dai, zan gaya muku wani abu mai burgewa sosai da ya faru a lokacin ambaliyar ruwa ta wannan karo, inda a tashar jirgin kasa dake birnin Zhengzhou, mamakon ruwan sama ya haddasa katsewar wutar lantarki, lamarin da ya hana jiragen kasa tafiya, da sanya fasinjoji tsayawa a cikin duhu a tashar. A wannan lokaci, wata kungiyar makada ta makarantar firamare dake cikin tashar ta fara yin wani kida mai nuna kishin kasa, inda kidan mai dadin ji ya kwantar da hankalin mutane, kana mutanen ma sun fara yin amfani da wayar salula da tocila don samar da haske ga yara makada.

Duk lokacin da ake gamuwa da matsala, nan take ake fara hadin gwiwa sosai cikin al’umma, wannan wani babban ruhi ne dake cikin al’adun mutanen kasar Sin. (Bello Wang)

Bello