Ma’aikatar wajen Sin: Tattaunawar Sin da Amurka a Tianjin ta gudana ba tare da wata rufa-rufa ba
2021-07-26 19:26:04 CRI
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, gabatarwa da aka yi a tattaunawar da kasashen Sin da Amurka suka yi Litinin din nan, ta fayyace komai ba tare da wata rufa-rufa ba, an kuma karfafa fahimtar matsayin ko wane bangane, yayin da tattaunawa da gaba, za ta karkata ga bunkasa hadin gwiwa mai tsafta tsakanin kasashen biyu.
Zhao Lijian ya bayyana haka ne, yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, lokacin da yake amsa tambayar cewa, a lokacin tattaunawa tsakanin sassan biyu, kasar Sin ta fuskanci matsaloli a hadin gwiwar dake tsakaninsu, inda ya yi karin haske game da halaye da matsayin kasar Sin, game da raya alakar sassan biyu bisa gaskiya da yin komai a bayyane.
Zhao ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da yadda Amurka ke tsoma baki a harkokin cikin gidanta da ma illata moriyar kasar Sin. A don haka, ta bukaci Amurka da ta gyara kura-kuranta. Haka kuma sassan biyu, sun yi musayar ra’ayoyi mai zurfi kan batutuwa da dama dake shafarsu.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)