Hussaini Abdullahi Umar: Akwai hadin-gwiwa mai kyau tsakanin Najeriya da Sin a bangaren inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma
2021-07-27 14:34:15 CRI
Hussaini Abdullahi Umar, dan Najeriya ne wanda a yanzu haka yake karo ilimi a jami’ar Central South dake birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin.
A zantawar da Murtala Zhang ya yi da shi, malam Hussaini Umar ya bayyana dalilin da ya sa ya zo kasar Sin don yin karatu, da ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu tsakanin Najeriya da Sin. Har wa yau, ya ce kasashen biyu suna yin hadin-gwiwa mai kyau a fannin inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, musamman hanyoyi da layin dogo da sauransu.
Har wa yau, a matsayinsa na wani malami dake aiki a jami’ar ABU Zariya, ya ce yana fatan amfani da ilimin da ya samu a kasar Sin wajen bada gudummawa ga gina kasarsa Najeriya.
A karshe, malam Hussaini Umar ya yi kira ga mutanen Najeriya da su jajirce wajen aiki da karatu. (Murtala Zhang)