logo

HAUSA

Xi ya bukaci a bude sabon shafin bunkasuwar jihar Tibet cikin zaman lumana

2021-07-23 21:40:29 CRI

Xi ya bukaci a bude sabon shafin bunkasuwar jihar Tibet cikin zaman lumana_fororder_hoto

A lokacin da ake murnar cika shekaru 70 da samun ‘yancin kan jihar Tibet cikin zaman lafiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a jihar, domin ganawa da al’ummomi da jami’an kabilu daban daban na jihar Tibet, tare da yi musu fatan alheri.

Xi Jinping ya ce, cikin shekaru 70 da suka gabata, bisa jagorancin kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, da goyon bayan dukkanin al’ummomin kasar Sin, da kuma kokarin da dukkanin jami’ai da al’ummomi na jihar Tibet suka yi, an samu gagarumin ci gaba a fannin raya zaman takewar al’umma da tattalin arzikin jihar Tibet, yayin da aka kyautata zaman rayuwar al’umma bisa dukkanin fannoni.

Lamarin da ya nuna cewa, in babu jagorancin JKS, ba za a samu bunkasuwar jihar Tibet, da ma kasar Sin baki daya ba. Manufofin da JKS ta tsara domin raya jihar Tibet sun yi daidai, sun kuma dace da halin da jihar take ciki kwarai da gaske. (Maryam)