logo

HAUSA

Bai kamata a ba da kai ga siyasa ba wajen binciken asalin kwayar cutar COVID-19

2021-07-23 11:22:01 CRI

A kwanan baya, kungiyar lafiya ta kasa da kasa WHO ta fitar da shirin aikin binciken gano asalin kwayar cuar COVID-19 a mataki na biyu. Bisa shirin, wai “kwayar cutar ta salule ne daga dakin gwaji na kasar Sin sakamakon karya ka’idojin yin aikin gwaji”, don haka, aka sanya shi zama daya daga cikin muhimman sassa na binciken da za a yi. Amma wannan ra’ayi bai yi daidai da sakamakon da kungiyar WHO ta fitar a watan Maris na bana ba, bayan da kwararrunta suka gudanar da bincike a dakin gwaji na kasar Sin a farkon bana. Bisa sakamakon da ta fitar a watan Maris na bana, an nuna cewa, “ba zai yiyuwa kwayar cutar ta bulla daga dakin gwaji ba.”

Bai kamata a ba da kai ga siyasa ba wajen binciken asalin kwayar cutar COVID-19_fororder_210723-rahoto-Sanusi Chen-hoto1

Abubuwan gaskiya su ne shaidu mafi kyau. Kawo yanzu, duk wanda yake aiki a dakin binciken kwayoyin halittu na Wuhan bai kamu da cutar COVID ba. Haka kuma ba a taba yin nazarin kwayoyin halittu irin na Korona a wannan daki ba, balle a hada su. Sakamakon haka, ina batun “salulewar kwayar cutar sakamakon karya ka’idojin yin aikin bincike” yake? Sanin kowa ne cewa, wasu ra’ayoyin dake cikin shirin yin bincike a mataki na biyu da WHO ta fitar ba su yi daidai ba. Wannan ya shaida cewa, yanzu ’yan siyasa sun tsoma baki a aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19.

Abu mafi muhimmanci shi ne, kawo yanzu kwararrun WHO sun riga sun yi bincike a kasar Sin har sau biyu, har ma sun riga sun gudanar da bincike a dakin nazarin kwayoyin cututtuka na Wuhan kamar yadda suke so. Bisa binciken da suka yi ne, sun fitar da sakamako cewa, ba zai yiyu kwayoyin cuta su sulale daga dakin gwaji na kasar Sin ba. Wannan sakamako, ba zai taba sauyawa ba har abada bisa ilmin kimiyya.

Yanzu ra’ayin “kwayar cutar Korona ba ta da alaka da dakin gwaji na Wuhan”, ya samu amincewar kwararru a duk fadin duniya. A ran 5 ga watan Yulin bana, kwararru 24 wadanda suka shahara a duniya wajen nazarin kwayoyin cuta, sun wallafa bayanansu a jaridar kiwon lafiya ta “The Lancet”, cewar kawo yanzu babu wata shaidar da ke iya goyon bayan ra’ayin “kwayar cutar Korona ta sulale ne daga dakin gwaji na Wuhan”. Sannan a ran 7 ga watan Yulin bana, wasu masu nazarin kimiyya na kasashen Amurka da Burtaniya da Australiya, su ma sun wallafa bayanansu a shafin intanet na Zenodo, inda suka nuna cewa, “babu shaidar dake nuna cewa, kwayar cutar Korona ta sulale ne daga dakin gwaji na Wuhan”, “babu shaidar dake nuna cewa, wadanda suka kamu da cutar a farkon lokaci suke da alaka da dakin gwaji na Wuhan”, “Babu shaidar dake nuna cewa, dakin gwaji na Wuhan yana da burbushin cutar kafin barkewarta a duk duniya.”

Bai kamata a ba da kai ga siyasa ba wajen binciken asalin kwayar cutar COVID-19_fororder_210723-rahoto-Sanusi Chen-hoto2

A bayyane take cewa, dukkan shaidun da aka samu yanzu sun bayyana cewa, kwayoyin cutar COVID-19 sun bullo a wurare da yawa a duk fadin duniya kafin a san lokacin bullarta. Alal misali, a cikin wani rahoton bincike da hukumar nazarin harkokin kiwon lafiya ta kasar Amurka ta fitar a watan Yunin bana, ya nuna cewa, kwayar cutar COVID-19 ta yadu a kasar Amurka a watan Disamban shekarar 2019. A watan Nuwamban shekarar 2019, a cikin samfurin ruwan dagwalo da aka samu a wani birnin kasar Brazil, an samu wani abu mai alaka da kwayar cutar COVID-19. A kwanan baya kuma, cibiyar nazarin ciwon sankara ta Milan ta kasar Italiya ta fitar da sabon sakamakon nazari cewa, mai yiyuwa ne kwayar cutar COVID-19 ta bullo a kasar Italiya a watan Oktoban shekarar 2019.

Wadannan shaidu sun bayyana cewa, asalin kwayar cutar COVID-19 ya kasance a wurare daban daban. Sabo da haka, ya zama wajibi a yi bincike a wurare daban daban a duk fadin duniya.

Alal misali, ya zama dole a yi bincike a kasar Amurka, wato “kasar ta gaza wajen tinkarar cutar a duk duniya.” Idan har ya zama dole a yi bincike a dakunan gwaji, to, ya kamata yanzu a gudanar da bincike a dakin nazarin kwayoyin hallitu na Fort Detrick da “cutar numfashi ta huhu” da ta bullo a yankunan dake kusa da dakin gwaji na Fort Detrick, kuma har yanzu ba a san dalilin da ya sa aka samu wannan cuta ba. A don haka, ya zama wajibi su zama muhimman sassan da WHO za ta gudanar da irin wannan bincike a mataki na biyu.

Kwayoyin cuta tamkar abokan gaban daukacin bil Adama ne. Kasashen duniya ba za su yi nasara ba, sai sun tinkare su cikin hadin gwiwa. Kawo yanzu, kasashe 55 sun rubuta wa babban sakataren WHO wasiku, inda suka nuna goyon bayansu na gudanar da aikin binciken gano asalin kwayoyin cutar a duk fadin duniya, amma ba su yarda a siyasantar da aikin ba. Wannan ra’ayoyi ne na galibin kasashen duniya. Aikin binciken gano asalin kwayoyin cutar, aiki ne na kimiyya, idan an ba da kai ga siyasa wajen binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19, hakika za a kawo illoli kwarai ga duniya baki daya. (Sanusi Chen)