logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya yi rangadi kan layin dogo mai aiki da wuta na farko a yankin Tibet

2021-07-23 11:30:35 CRI

Shugaban kasar Sin ya yi rangadi kan layin dogo mai aiki da wuta na farko a yankin Tibet_fororder_3c6d55fbb2fb431675aeedd384809f2b08f7d397

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tafi birnin Linzhi ta jirgin kasa a jiya, inda ya yi rangadi kan layin dogo mai aiki da wutar lantarki na farko da aka shimfida a kan babban tudu, wato layin dogon dake tsakanin Linzhi da Lhasa.

Wannan layin dogo yana kan kwarin dake kudu maso gabashin yankin Tibet dake tsakanin tsaunukan Gangdis da Himalayas a kan tudun Qinghai-Tibet. Aikin shimfida layin dogo a wurin na da wahala, inda aka kwashe shekaru 6 ana gina wannan layin dogo. A ranar 25 ga watan Yunin bana, aka kaddamar da layin dogo mai tsawon kilomita 435.48 da tasoshi 9 dake tsakanin Lhasa da Linzhi, yayin da saurin tafiyar jirgin kasan ya kai 160 kilomita kowace awa. Ana iya tafiya tsakanin Lhasa zuwa Linzhi cikin sa’o’i 3 da mintoci 29 kadai.

Ban da wannan kuma, wannan layin dogo na hade da layin godon dake tsakanin Lhasa da Rikaze da wanda ke tsakanin Qinghai da Tibet wato layin dogo na Qingzang, kuma wani muhimmin bangare ne cikin layin dogon dake tsakanin Sichuan da Tibet wato Chuangzang da ake kokarin ginawa yanzu da kuma layin dogon dake tsakanin Yunnan da Tibet wato Dianzang da ake shirin ginawa. Amfani da wannan layin dogo ya kawo karshen rashinsa a yankin kudu maso gabashin Tibet, da ma kyautata halin da yankin ke ciki a wannan fanni da kuma inganta zirga-zirga da sufuri a yankin. (Amina Xu)