logo

HAUSA

Uganda ta yabawa taimakon da Sin ke ba ta wajen bunkasa kayayyakin more rayuwa

2021-07-22 10:18:05 CRI

Uganda ta yabawa taimakon da Sin ke ba ta wajen bunkasa kayayyakin more rayuwa_fororder_210722-Ahmad-Uganda

Ministan harkokin wajen kasar Uganda Jeje Odongo, ya yabawa kasar Sin bisa yadda take ci gaba da taimakawa kasar ta gabashin Afrika a fannin bunkasa ci gaban kayayyakin more rayuwa.

Odongo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar takardun kama aikin sabon jakadan kasar Sin a Uganda Zhang Lizhong, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana cikin wata sanarwa.

Ministan ya yaba da dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar ta nahiyar Asiya, inda ya bayyana cewa dangantaka ce mai cike da tarihi, kana dangantakar ta samu bunkasuwa zuwa matsayin cikakkiyar dangantaka.

Ministan ya ce kasar Uganda tana sha’awar bunkasa mu’amalar cinikayya da kasar Sin da kuma gabatar da tsarin sufurin jiragen sama na kai tsaye tsakanin kasar Uganda zuwa birnin Guangzhou na kasar Sin.

Ambasada Zhang ya ce, Uganda tana kara zurfafa alakarta da kasar Sin a fannonin siyasa, tsaro, tattalin arziki, al’adu da fannin kimiyya.

Tun bayan barkewar annobar COVID-19 a kasar Uganda a watan Maris na shekarar bara, kasar Sin ta bayar da gudunmawar kayayyakin kiwon lafiya ga kasar Uganda. Sannan kuma kasar Sin ta bayar da gudunmawar alluran riga-kafin COVID-19 kimanin 300,000 ga kasar Uganda. (Ahmad)