Kara kalmar “Tare” cikin babban taken wasannin Olympics na da ma’ana ta musamman
2021-07-22 14:24:22 CRI
Gobe Jumma’a ne, za’a kaddamar da gasar wasanin motsa jiki na Olympics na lokacin zafi karo na 32 a birnin Tokyo na kasar Japan, gasa mafi kasaita a fadin duniya. Wani babban al’amarin da ya jawo hankalin al’umma shi ne, a yayin cikakken zama na 138 na kwamitin shirya gasar da aka yi kwanan nan, an kara kalmar “tare” wato “together” a Turance cikin babban taken wasannin Olympics, wanda a baya jigon ke zama “ci gaba, kuzari da karfi”.
Babban taken da ake kira “Ci gaba, kuzari da karfi” ko kuma “Faster, Higher, Stronger” a Turance, dan kasar Faransa Pierre De Coubertin ne wanda ake kira “uban wasannin Olympics na zamani” ya bayyana shi yayin da aka kafa kwamitin shirya gasar wasannin Olympics a shekara ta 1894, daga baya aka shigar da shi a hukunce a gasar wasannin Olympics na Paris a shekara ta 1924. Babban taken ya shawarci ’yan wasan motsa jiki daga kasa da kasa su jajirce wajen shiga gasa ba tare da nuna kasala ba. Bayan shekaru 100, wato a zamanin yau, an kara kalmar “tare” cikin taken, abun da ya sanya sabuwar ma’ana cikin wasannin Olympics, da bayyana kyakkyawan fata na daukacin al’ummun duniya, wanda ke da muhimmiyar ma’ana ga tinkarar kalubaloli iri daban-daban da duniya take fuskanta
Kwamitin shirya wasannin Olympics ya kawo sauyi ga babban taken wasannin, wanda ke da tarihi na shekaru 100, abu ne da ya dace ya yi. Duba da illolin da cuar COVID-19 ke haifarwa, ya sa an dage wasannin Olympics na Tokyo har tsawon shekara guda. Kuma wasannin Olympics na Tokyo na fuskantar matsalar rashin amincewa daga bangarori daban-daban, matsalar da sannu a hankali ta zama rashin amincewar da ake wa kwamitin shirya wasannin Olympics gami da gasar wasannin Olympics ita kanta, har ma bambancin ra’ayi da rikici na kara kunno kai. A sabili da haka, ana iya fahimtar dalilin da ya sa shugaban kwamitin wato Thomas Bach ya ce ya dace a sabunta babban taken Olympics bisa canjin yanayi, kuma akwai bukatar a kara maida hankali kan hadin-gwiwa a halin yanzu.
A halin yanzu cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duniya, kuma farfadowar tattalin arizkin duniya na fuskantar babbar barazana, har akwai wasu ‘yan siyasar kasashen yamma wadanda suke yunkurin tada zaune-tsaye da yin fito-na-fito tsakanin kasa da kasa don kawowa duniya baraka, abun da ya haifar da mummunan tasiri kai-tsaye ga akidar wasannin Olympics na zamani, wato “karfafa zaman jituwa tsakanin al’umma, raya kyakkyawar duniya cikin hadin-gwiwa”.
A halin yanzu, al’ummomin duniya na bukatar tallata akidun wasannin Olympics fiye da kowane lokaci a baya, wato akidun da suka shafi kara ci gaba, da sada zumunta da mutunta juna da kuma karfafa hadin-gwiwa, kuma suna bukatar a kawar da duk wani abin da ka iya kawo cikas da kawar da rikici ta hanyar halartar wasanin motsa jiki. Hakika, lokacin da ’yan wasan motsa jiki daga kasashe daban-daban suke haye wahalhalun dake tattare da annobar, har suka hadu a Tokyo, za’a iya shaida babbar ma’anar Olympics, wato hada kan duk duniya.
Har wa yau, sanya kalmar “tare” cikin babban taken Olympics zai karfafa al’ummomin duniya gwiwar shawo kan kalubaloli da ka iya kunno kai a nan gaba. Shugaban kwamitin shirya gasar Olympics Thomas Bach ya ce, al’ummar duniya na dogara da juna, babu wani mutum ko wata kasa da zai iya tinkarar kalubale ita kadai. Kawo sauyi ga babban taken Olympics shi ne domin fadakar da al’umma kan cewa, ya kamata a gina al’umma mai makoma ta bai daya, sa’annan ko a fannin kiyaye tsaro da lafiyar al’umma, ko kuma a fannin tinkarar matsalar sauyin yanayi, hadin-gwiwa tamkar wani makami mafi amfani.
A bangaren kasar Sin ma, a matsayinta na kasar da za ta karbi bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu a shekara ta 2022, kasar Sin ta tura wata tawaga mai girma zuwa gasar da ba’a taba ganin irin ta ba a tarihi, tare kuma da daukar matakan kandagarkin cutar mafi tsauri. Wannan shi ne muhimmin mataki da kasar Sin ta dauka domin tabbatar da sabon babban taken wasan Olympics, kana sabuwar gudummawa ce da kasar ta bayar wajen inganta hadin-gwiwar kasa da kasa da tinkarar kalubale kafada da kafada. (Murtala Zhang)