logo

HAUSA

Gine gine 800 ne ke fuskantar barazana daga gobarar daji a arewacin California

2021-07-21 09:50:17 CRI

Gine gine 800 ne ke fuskantar barazana daga gobarar daji a arewacin California_fororder_1

Zuwa jiya Talata, gobarar daji da ta tashi a ranar 13 ga wata a gundumar Butte na arewacin California, na ci gaba da ruruwa, inda take barazana ga gine-gine ko kayayyaki sama da 800.

Rahoto na baya-bayan nan da Inciweb mai yada bayanan hadari tsakanin jihohi ya fitar, ya ce gobarar da aka yi wa lakabi da Dixie, ta kona filayen da fadinsu ya kai murabbin kilomita 242.8, kana an shawo kan kaso 15, sai dai sama da gine-gine 800 ne ke fuskantar barazana daga gobarar bayan ta talalata wasu guda 2.

Yanzu haka, an tura jami’an kwana-kwana 2,409 domin kashe gobarar Dixie tare da injuna 141 da jiragen masu saukar ungulu 23 da bulldoza 49. Tuni dai cibiyoyin ba da daukin gaggawa na gundumomin Plumas da Butte ke zaune cikin shiri, inda jami’ai suka isa wurin domin taimakawa hukumomi yayin da suke tunkarar ayyukan gaggawa. (Fa’iza Mustapha)