logo

HAUSA

Uganda za ta karbi kimanin alluran COVID-19 miliyan 12.3 ya zuwa farkon shekarar 2022

2021-07-21 10:06:07 CRI

Uganda za ta karbi kimanin alluran COVID-19 miliyan 12.3 ya zuwa farkon shekarar 2022_fororder_210721-Ibrahim4-Uganda

Rahotanni daga kasar Uganda na cewa, nan da farkon shekarar 2022, kasar tana sa ran karbar a kalla alluran riga kafin COVID-19 miliyan 12.3. Mai magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiyar kasar, Emmanuel Ainebyoona, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho jiya Talata cewa, za a shigo da alluran ne kashi-kashi.

Ya kara da cewa, ma’aikatar tana sa ran karbar allurai 286,080 na kamfamin AstraZeneca a karshen makon watan Yulin da muke ciki, baya ga tallafin alluran riga kafin kamfanin Sinovac guda 300,000 daga kasar Sin da su ma za ta karba a wannan lokaci, akwai kuma wasu alluran riga kafi na kamfanin AstraZeneca guda 688,800, da kasar take sa ran karba a watan Agusta dake tafe.

Ya zuwa yanzu dai, kasar Uganda ta yiwa sama da ’yan kasarta miliyan 1 alluran riga kafin, tun lokacin da ta kaddamar da shirin riga kafin a watan Maris din da ya gabata. (Ibrahim)