logo

HAUSA

Yau take babbar sallah a sassan duniya

2021-07-21 08:57:19 CRI

A yau Talata 20 ga watan Yuli, daidai da ranar 10 ga watan Zhul Hajj bisa kalandar musulunci, miliyoyin al’ummar musulmin duniya ke gudanar da bukukuwan babbar sallah, wadda daya ce daga muhimman ranekun ibada na mabiya addinin Islama.

Yau take babbar sallah a sassan duniya_fororder_210721世界21027-hoto3

Musulmi na gudanar da sallar Idin babbar sallah ne da hantsin wannan rana, kafin kuma su yanka dabbar layya, dake matsayin muhimmiyar ibada mai nasaba da ranar.

Kafin ranar babbar sallah, a jiya Litinin, mahajjata dake kasar Saudiyya, sun gudanar da tsayuwar Arafa, wadda ita ce ibada mafi muhimmanci a ibadun aikin Hajji. Mahajjatan sun shafe sa'o'i da dama a filin Arfa, wanda shi ne filin da Manzon Allah (SWT) ya yi huɗubarsa ta ban kwana.

Yau take babbar sallah a sassan duniya_fororder_210721世界21027-hoto2

Kamar bara, a bana ma kasar Saudiyya ta taƙaita yawan Musulman da suka gudanar da aikin hajjin zuwa mutum 60,000 kacal, kuma mafi yawan su mazauna kasar ne, a maimakon mutum kusan miliyan uku da kan yi aikin Hajjin a duk shekara. Saudiyya ta dauki wannan mataki ne da nufin tabbatar da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

A nan ma kasar Sin, dubun dubatar musulmi sun gudanar da sallah a masallatai daban daban, tare da aiwatar da matakan da suka wajaba na ba da kariya daga kamuwa da cutar COVID-19, duk da cewa a yanzu ba a samun yaduwar cutar a cikin kasar.

Yau take babbar sallah a sassan duniya_fororder_210721世界21027-hoto4

Ana iya ganin musulmi sanye da kyawawan tufafi, suna gudanar da ibadu da hantsin wannan rana ta Talata, tare da sada zumunci, da yiwa juna fatan Alherin sake kewayowar wannan muhimmin biki.

Bikin babbar sallah na alamta fatan musulmi na samun yardar ubangiji, da rahama da wadata. Lokaci ne kuma na murna, da ke cike da nishadi da annashuwa. (Saminu, Ahmad)