logo

HAUSA

Kasashen Duniya Dake Goyon Bayan Adaci Da Gaskiya Kan Batun Gano Asalin Kwayar Cutar COVID-19 Na Kara Goyon Bayan Kasar Sin

2021-07-21 17:12:42 CRI

Kasashen Duniya Dake Goyon Bayan Adaci Da Gaskiya Kan Batun Gano Asalin Kwayar Cutar COVID-19 Na Kara Goyon Bayan Kasar Sin_fororder_FB3D5600-DA0F-4E94-B749-209062847600

Daga Amina Xu

Kwanan baya, babban jami’in WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a taron manema labarai cewa, yanzu duniya na kokarin tinkarar cutar COVID-19 tare da samun nasarori, inda ake sake mai da hankali kan aikin gano asalin kwayar cutar, saboda haka, yana fatan kasar Sin za ta sake bude kofarta don masanan hukumasu kawo mata ziyara a karo na biyu. Shin me ya sa ba za a gudanar da irin wannan bincike a sauran kasashe ba, a maimakon haka hukumar na shirin gudanar da bincike a kasar Sin a karo na biyu? A ran 30 ga watan Maris nabana, WHO ta gabatar da rahoton binciken da ta yi a kasar Sin a Geneva cewa, batun bullarkwayar cutar daga dakin gwaji ba zai yiwu ba. To, Me ya sa Tedros Adhanom Ghebreyesus ya musanta rahoton da hukumar ta fitar da kanta?

Rahotanni na cewa, bayan cikakken nazarin da masanan WHO suka yi a kasar Sin, sun gano cewa, ya zuwa yanzu babu shaidu dake bayyana cewa, kwayar cuta ta samo asali ne daga jemage ko sauran namun daji a kasar Sin. Kuma babu shaidu dake bayyana cewa, cutar ta barke a karshen rabin shekarar 2019. Amma, akwai shaidu da dama dake bayyana cewa, wannan cutar ta bulla ne a watanni 6 na karshen shekarar 2019 a kasar Amurka. Abin da ya nuna cewa, ba a Sin cutar ta samo asali ba. A sa’i daya kuma, kasashen duniya sun rika yin kira da a gudanar da bincike kan cibiyar nazarin kwayoyin hallitu ta Fort Detrick ta Amurka. Shin ko Amurka tana yunkuri dora laifi kan kasar Sin ne a daidai wannan lokaci da nufin boye wasu abubuwa? Idan WHO ta ce za ta gudanar da irin wannanbincike a Amurka, ko Amurkar za ta bude kofarta ba tare da boye-boye ba?

Wakilin kasar Austriliya Dominic Dwyer kana mamban tawagar masana kasa da kasa da WHO ta tura kasar Sin, don gudanar da aikin bincike gano asalin cutar a farkon bana, ya ceyin bincke a kasar Sin, shi ne matakin farko na aikin ganoasalin kwayar cutar, daga baya za a gudanar da irin wannan bincike a sauran kasashe. Baya ga kasar Sin, wajibi ne sauran kasashe a duniya su hada kai da WHO, don ganin gudanar da irin wannan bincike a kasashensu. Amma, Amurka ba ta bayyana ra’ayinta a fili game da wannan batu ga duniya ba, har ma tana yunkurin shafawa kasar Sin bakin fenti ta hanyar amfani da hukumar leken asiri. Game da haka, kasashe da al’ummar duniya ba su yarda da wannan wayo na Amurka ba.

Ba da dadewa ba da Tedros ya sanar da sake yi wa kasar Sin bincike, kasashe 48 sun mika masa wasikar nuna adawa, kuma ya zuwa ran 20 ga wata, kasashe 55 sun bayyana rashin jin dadinsu game da siyasantar da batun gano asalin kwayar cutar. To, ko wadannan kasashe suna goyon baya kasar Sin ne kawai a kan wannan batu ko a’a? Amsar ita ce, suna goyon bayan adalci da gaskiya! A cikin wasikar da wadannan kasashe suka mikawa Tedros, sun nuna cewa, Sin ta ba da babbar gudunmawa ga duniya wajen hana yaduwar cutar tun lokacin barkewarta, ban da wannan kuma, Sin ta zama abin koyi a fannin aikin kandagarki da fitar da allurar rigakafi da kuma taimakawa sauran kasashe gwargwadon karfinta. Ban da wannan kuma, masanin Amurka, kana babban mashawarcin fadar White House kan lafiya, Anthony Fauci, ya bayyana a ran 19 ga wata cewa, asalin kwayar cutar COVID-19 ka iya zama daga halitta. Goyon bayan da sauran kasashe ke baiwa kasar Sin nabayyana cewa, mai adalci zai samun goyon baya daga bangarori daban-dabankuma gaskiya kullum sunanta GaskiyaSai dai kuma, wasu ‘yan siyasa na baza jita-jitar cewa, kwayar cutar ta samo asali ne daga dakin nazarin hallitu, suna kokarin dora laifin kan wasu, amma, abin tambaya shi ne, me kasa za ta amfana da shi, idan ta boye wani abu game da cutar dake gagar Kwandila? Komai nisan dare, Gari zai waye (Amina Xu)