logo

HAUSA

Karya fure take bata ’ya’ya

2021-07-20 16:51:05 CRI

Karya fure take bata ’ya’ya_fororder_AA

Babban mashawarcin fadar shugaban kasar Amurka kan harkar lafiya Dr. Anthony Fauci, ya bayyana cewa, bayani mafi gamsarwa shi ne kwayar cutar COVID-19 ta samo asali daga dabbobi sannan ta yadu zuwa ga dan adam. A matsayinsa na kwararre kuma masani a fannin lafiya da nazarin cututtuka masu yaduwa, Anthony Fauci ya bayyana haka ne yayin da yake hira da gidan talabijin na CNN. Ba wannan ne karon farko da masana kiwon lafiya daga ciki da wajen Amurka ke bayyana makamancin zancen ba, wato musunta yuwuwar samun kwayar cutar daga dakin gwaji kamar yadda gwamnatin Amurka ke ikirari.

Shekara sama da 1 bayan sanar da bullar cutar a hukumance, har yanzu Amurka na kokarin alakanta ta da kasar Sin. Amurka na ikirarin cutar ta samo asali ne daga dakin gwaje-gwajen kwayoyin halittu na birnin Wuhan dake tsakiyar kasar Sin. Ai idan mai fada wawa ne, to mai sauraro ba wawa ba ne. Duk wanda ya san yadda gwamnatin kasar Sin take tafiyar da harkokinta da kuma naufofi, to ya kwan da sanin cewa ta kan mayar da hankali ne kan duk wani abu da zai kare muradun al’ummarta tare da kaucewa abun da zai jefa su cikin mawuyacin hali. Don haka, wani amfani kirkiro cutar zai yi wa al’ummar kasar Sin? idan ba a manta ba, bullar cutar ta tsayar da al’amura cak, ba a birnin Wuhan kadai ba, har da sauran sassan kasar Sin. Haka zalika, kamar sauran sassan duniya, ita ma kasar Sin ta ji a jikinta sanadiyyar barkewar cutar.

Maimakon gwamnatin Amurka ta mayar da hankali wajen kare al’ummarta da dakile cutar daga yaduwa zuwa sauran sassan duniya kamar yadda kasar Sin ta yi, sai ta mayar da hankalinta wajen siyasantar da batutuwan da suka shafi cutar, ciki har da matakan da Sin ta dauka na yaki da ita, lamarin da ya kai ga kisan dubban Amurkawa, inda miliyoyi kuma suka yi fama da cutar. Amurka ta yi wasarairai da rayukan jama’arta, tana kokarin tada fitina a kan abun da bata da shaidu ko hujja.

Shin kasar Sin ta yi laifi ne da ta fara sanar da gano cutar? Ai ba dan sanarwar da ta yi tare da ankarar da hukumomi ba, da illar da cutar za ta yi, ya tsallake tunanin dan Adam. Sanar da bullar cutar da Sin ta yi ya samar da dama da lokaci har ma da matakan tunkarar cutar.

Ba Anthoony Fauci ne kadai ya musanta batun kirkiro cutar a dakin gwaji ba, har ma da Paul Offit, mamban kwamitin kula da ingancin abinci da magunguna na kasar, inda ya ce abu ne mara yuwuwa a ce cutar ta samo asali daga dakin gwaji.

Kamar yadda Matthew Kavangh, daraktan cibiyar nazarin manufofin kiwon lafiya da harkokin siyasa ta duniya dake Jami’ar Georgetown na Amurkar ya bayyana, idan har gwamnatin Amurkar na son gano asalin cutar, to masana kimiyya da cibiyoyi da hukumomin lafiya ne ya kamata su yi bincike amma ba hukumar leken asiri ba. Wannan kadai ya isa nuna kokarin Amurka na siyasantar da batun cutar da kokarinta na ganin baiken kasar Sin ko ma shafa mata bakin fenti a idon duniya. karya fure take bata ‘ya’ya, kuma da sannu Amurka za ta ji kunya muddun ta ci gaba da tafiya akan wannan hanyar mara bullewa. Maimakon zubar da kima da darajar kasar Sin, ita ce girmanta zai zube. (Fa'iza Mustapha)