logo

HAUSA

Balarabe Shehu Ilelah: Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta jagoranci kasar wajen samun dimbin nasarori

2021-07-20 16:35:29 CRI

Balarabe Shehu Ilelah: Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta jagoranci kasar wajen samun dimbin nasarori_fororder_微信图片_20210720163449

Kwanan nan ne, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da malam Balarabe Shehu Ilelah, babban darektan hukumar kula da harkokin yada labarai ta kafofin rediyo da talabijin ta Najeriya ko kuma NBC a takaice, wanda ya shafe shekaru da dama yana zaune a kasar Sin, inda ya bayyana ra’ayinsa kan muhimmiyar rawar da jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ta taka, tun farkon kafuwarta har zuwa yanzu, wato lokacin da aka cika shekaru 100 da kafuwarta, musamman a fannonin da suka shafi kyautata rayuwar al’umma, raya tattalin arziki, yaki da cutar mashako ta COVID-19 da sauransu.

Malam Balarabe ya kuma yi tsokaci kan sirrin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a fannin jagorantar al’ummar kasar wajen samun dimbin nasarori.

A karshe, malamin ya bayyana fatansa na ci gaba da inganta hulda da dankon zumunta tsakanin Sin da Najeriya da ma sauran kasashen Afirka. (Murtala Zhang)