logo

HAUSA

Algeria za ta bunkasa hadin gwiwa da Sin karkashin shawarar BRI

2021-07-20 12:58:05 CRI

Algeria za ta bunkasa hadin gwiwa da Sin karkashin shawarar BRI_fororder_210720-Faeza 1-Aljeriya

Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune, ya bayyana a jiya cewa, kasarsa ta shirya zurfafa hadin gwiwa da Sin a fannoni da dama karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

Shugaban na Algeria ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da mamban majalisar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi dake ziyara a kasar.

Da yake bayanai game da daddadiyyar dangantakar abota da aminci dake tsakanin kasashen biyu, shugaba Tebboune ya ce tun da kasar ta samu ‘yancin kanta, manufar kasar Sin daya taka a duniya bata taba sauyawa ba.

Yayin da kasashen biyu suka shiga wani sabon matakin ci gaba, ana fatan za su zurfafa hadin gwiwa a fannonin da suka shafi tattalin arziki da cinikayya da zuba jari da makamashi da hakar ma’adinai da ginin ababen more rayuwa karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, domin samun ci gaba na bai daya, wanda kuma zai amfanawa sauran kasashe masu taowa.

Shugaban na Algeria ya kuma taya Sin murnar cika shekaru 50 da dawo da kujerarta a MDD, yana mai cewa Algeria na sa ran Sin za ta kara taka rawa a harkokin da suka shafi duniya da kuma inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinta da ma duniya baki daya.

A nasa bangaren, Wang Yi ya mika sakon gaisuwa daga shugaba Xi Jinping zuwa da shugaba Tebboune.

Ya ce shekaru 50 da suka gabata, Algeria tare da sauran kasashe masu tasowa sun yaki matsin lamba da katsalandan, suka bada cikakkiyar goyon baya wajen dawo da halaltacciyar kujerar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a MDD.

Kuma shekaru 50 bayan nan, gashi ya koma kasar, domin murnar wannan gagarumin batu, da kuma bayyana godiya ga abokai ‘yan Algeria.

Ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Algeria wajen kare halaltattun hakkoki da muradun kasashe masu tasowa da kuma daukaka adalci a duniya.

Har ila yau, ya yi alkawarin Sin za ta ci gaba da samar da alluran riga kafin cutar COVID-19 ga Algeria da inganta hadin kansu kan samar da riga kafin domin gaggauta shawo kan annobar a kasar. (Fa’iza Mustapha)