logo

HAUSA

Bai Kamata A Bar Jaki Ana Dukan Teki Ba

2021-07-19 16:34:39 CRI

Bai Kamata A Bar Jaki Ana Dukan Teki Ba_fororder_微信图片_20210719160303

Daga Ahmad Fagam

A dai dai lokacin da duniya ke cikin halin tsaka mai wuya dangane da yaduwar sabuwar cutar COVID-19 nau’in Delta wacce masana suka bayyana ta da cewa tana da hadarin gaske, babban abin da ya fi dacewa shi ne al’ummun kasa da kasa su hada karfi da karfe domin yiwa annobar rubdugu da nufin karya lagon cutar. Sai dai abin takaici shi ne, a maimakon hakan, wasu kasashe sun fi mayar da hankali ne kan batun siyasantar da aikin gano asalin cutar. Ko da a karshen wannan mako, sai da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce kasarsa tana kira ga sassa masu ruwa da tsaki da su dakatar da siyasantar da aikin gano asalin cutar COVID-19, da dora laifi kan wasu, su kuma kaucewa gurgunta yunkurin kasa da kasa na hadin gwiwar binciko asalin annobar. Kakakin ya gabatar da wannan kira ne bayan da wakilan wasu kasashe 44 suka gabatar da wasikar hadin gwiwa, ga babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Mr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, da kuma wasu wasiku daban daban da kasashe 4 suka rubutawa babban daraktan WHO game da wannan batu. Da yake karin haske kan wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Sin ya ce, tun farkon bullar wannan annoba, Sin ta rungumi matakai na kimiyya, da kwarewa, da jajircewa wajen ganin an gano asalin annobar. Kaza lika, Sin ta zamo a sahun gaba wajen tabbatar da nasarar hadin gwiwar sassan kasa da kasa da WHO. A hannu guda kuma, kasar na aiwatar da dukkanin matakai a bude, matakan da kuma suka samu matukar amincewa tsakanin kwararru na kasa da kasa. To sai dai kuma duk da haka, a wasu lokuta, wasu kasashe kalilan karkashin jagorancin Amurka, suna nunawa wasu sassa kyama, ta hanyar fakewa da wannan batu, suna siyasantar da aikin binciken asalin cutar. Jami’in ya ce, irin wadannan dabi’u sun yi matukar gurgunta kokarin da sassan duniya ke yi, na gudanar da hadin gwiwar binciko asalin cutar. Daga nan sai jami’in ya ce bisa adalci, mafi yawan kasashe masu tasowa sun nuna goyon bayansu ga wannan wasika, suna masu fatali da yunkurin siyasantar da wannan muhimmnin aiki. Kasashe da dama sun amince cewa, kalubalantar kimiyya, ko sauya gaskiya da wasu kasashe kalilan suke yi karkashin jagorancin Amurka bai dace ba. Kuma matsayar mafi yawan kasashen duniya ta shaida cewa, duniya na goyon bayan adalci, gaskiya da bin doka. A maimakon siyasantar da wannan batu ya fi kyau a kara kaimi tare da yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin ganin bayan wannan annoba kamar yadda har kullum kasar Sin ke nanata wannan aniyar domin a gudu tare a tsira tare. Alal misali, koda a lokacin da yake halartar kwarya-kwaryar taro na shugabannin APEC ta kafar bidiyo a karshen mako, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada matsayin kasar Sin, da matakan da za ta dauka wajen goyon bayan kasashen duniya a fannin yaki da annobar, ciki har da ba da tallafin kudi na dala biliyan 3 don taimakawa kasashe masu tasowa a cikin shekaru uku masu zuwa, da kuma bada goyon baya ga samun shaidar ’yancin mallakar fasaha ta alluran riga-kafin COVID-19, kana kasar Sin a shirye take ta shiga a dama da ita cikin ayyukan hadin gwiwar domin cimma nasarar kawar da wannan annoba wacce ta firgita kafatanin al’ummar duniya. (Ahmad Fagam)