logo

HAUSA

Tawagar ‘yan wasan Sin tana fatan gudanar da gasar Olympics ta Tokyo cikin yanayi mai kyau

2021-07-19 14:15:16 CRI

Tawagar ‘yan wasan Sin tana fatan gudanar da gasar Olympics ta Tokyo cikin yanayi mai kyau_fororder_hoto

Yau Litinin, babban sakataren tawagar ‘yan wasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, a halin yanzu, ‘yan wasan kasar Sin suna sauka kasar Japan bi da bi domin halartar gasar wasannin Olympics, kuma, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa domin nuna goyon baya ga kasar Japan wajen gudanar da gasar ta wannan karo lami lafiya.

Kuma ya jaddada cewa, kasar Sin tana godiya ga kasar Japan dangane da kokarin da ta bayar wajen gudanar da gasar wasannin Olympics, musamman a halin yanzu da ake fuskantar matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a kasa da kasa.

Sa’an nan, ya jaddada cewa, ‘yan wasan kasar Sin za su bi ka’idojin da kwamitin wasannin Olympics na birnin Tokyo ya tsara domin kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19 yadda ya kamata. Kana, za su yi hadin gwiwa da tawagogin ‘yan wasa na kasashen duniya, domin nuna goyon baya ga kwamitin gasar wasannin Olympics na birnin Tokyo, ta yadda za a yi nasarar gudanar da gasar ta wannan karo kamar yadda ake fata. (Maryam)