Amurka ta zubar da alluran rigakafi tare da nauyin da ke bisa wuyanta cikin kwandon shara
2021-07-18 22:19:30 CRI
“Zuwanmu kasar Amurka ba don neman cimma ‘mafarkin kasar’ ba, amma don neman cimma ‘mafarkin samun rigakafi’”, in ji wani dan kasar Peru, wanda kwanan baya ya je kasar Amurka don neman a yi masa rigakafin cutar Covid-19.
Yanzu haka, Peru tana sahun gaba wajen samun yawan wadanda suka mutu sakamakon annobar, inda daga cikin ‘yan kasar dubu 100, akwai 596 da suka mutu a sakamakon cutar. Duk da haka, kasar ta kasa samun isashen rigakafin cutar, abin da ya sa‘yan kasar ba yadda za su yi sai su yi kokarin zuwa wasu kasashe, musamman ma kasar Amurka, wadda ta tara alluran rigakafin cutar masu yawan gaske, don neman a yi musu rigakafi. Ban da Peru, akwai kuma kasashen Latin Amurka da yawa da al’ummunsu ke kokarin zuwa Amurka, lamarin da ya sa kudin jirgi na zuwa Amurka ma ya karu da yawa. Amma, ba kowa ke iya biyan kudin ziyarar ba.
A hakika, hakan ya faru ne a sakamakon rashin adalci wajen samar da rigakafi a sassan duniya. Alkaluman da hukumar lafiya ta nahiyar Amurka ta fitar sun yi nuni da cewa, duk da cewa an yi wa al’ummun nahiyar miliyan 400 rigakafi, amma akasarinsu suna kasar Amurka, a yayin da kaso 3% na mutanen kasashen Latin Amurka ne kawai aka yi musu rigakafin. Sai dai a yayin da Peru da sauran kasashen Amurka suke fama da karancin samun rigakafi, ga shi Amurka ta tanadi allurai masu tarin yawa, duk da wa’adin da yawa daga cikinsu na kokarin karewa, amma ba ta son samar da gudummawa ga makwabtanta. Lalle, watakila“rashin adalci” ne a fadi haka, da a ce a makon da ya wuce ne, kasar ta samar da allurai 80 ga kasar Trinidad and Tobago da ke tsakiyar nahiyar Amurka. Haka ne, ban yi kuskure, allurai 80 ne kawai ta samar, kwatankwacin al’ummar kasar miliyan 1.4, me allurai 80 zai yi musu?
Yadda kasar Amurka din ke nuna ra’ayin son kai ya sa jaridar Washington Post ta kasa hakuri, wadda har ta wallafa wani sharhi a kwanan baya, inda take zargin cewa, Amurka ta tara alluran rigakafi masu dimbin yawa. Sharhin ya bayyana cewa, dalilin da ya sa Amurka ta tanadi allurai masu tarin yawa shi ne sabo da tana son cimma burin da ta tsara a baya, na yiwa kaso 70 cikin 100 na baligan kasar alluran riga kafin a kalla daya kafin ranar 4 ga watan Yuli, wanda abu ne mai matukar wahala. Yanzu haka ma, akwai miliyoyin alluran da wa’adinsu ke kokarin karewa da Amurkar ta boye, kuma babu abin da za a yi da su sai dai a zubar da su a kwandon shara. Sharhin ya kuma yi nuni da cewa, yadda Amurka ta gaza matuka wajen magance yanayin cutar, shi ne ta mai da hankali kawai kan yanayin annobar a cikin gida, kuma ta yi watsi da barazanar da kasashen ketare suke fuskanta.
An ce, yawan al’ummar kasar Amurka ya kai miliyan 330, adadin da ya dau kaso 4% na al’ummar duniya baki daya, sai dai kasar ta yi kokarin sayen alluran rigakafi biliyan 2.6, adadin da ya kai kaso 1/4 na gaba dayan alluran da aka samar a duniya. A sa’i daya kuma, akwai kasashe sama da 10 a duniya da suke tsananin fama da karancin rigakafin, inda ko likitocin da ke ceton masu cutar ma sun kasa samun rigakafin.
Lalle, a yayin da cutar Covid-19 ke ci gaba da yaduwa a duniya, yadda Amurkar take tara alluran rigakafi fiye da kima ya kasance tamkar ta kashe mutane masu bukata a kasashe masu tasowa. Daidai kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mr.Zhao Lijan ya fada a yayin da ya mai da martani kan sharhi na jaridar Washington Post, “kasar Amurka ta zubar da alluran da wa’adinsu ta kare cikin kwandon shara, tare kuma da nauyin da ke bisa wuyanta.”
Kwatankwacin yadda Amurka ke yi, kullum kasar Sin na kokarin taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun rigakafi cikin sauki, duk da al’ummarta masu yawa wadanda su ma suke bukatar rigakafi. Ya zuwa yanzu, kasar ta Sin ta riga ta samar da alluran rigakafi kimanin miliyan 500 ga kasashe da kungiyoyin duniya sama da 100, adadin da ya kai kimanin kaso 1/6 na alluran da aka samar a duniya baki daya, kuma hakan ya sa ta zama kasar da ta fi yawan samar da rigakafi ga kasashe masu tasowa. Ban da haka, kasar Sin tana kuma kokarin hadin gwiwa da kasashe masu tasowa ta fannin samar da rigakafin. Kada kuma mu manta, a watan da ya wuce ne, kasar ta samar da allurai dubu 100 ga kasar Trinidad and Tobago.
Kwanan nan, Maitreya Bhakal, dan jaridar kasar Indiya ya wallafa wani sharhi ta kafar RT, inda ya ce kasar Sin ta samar da wata hanyar rigakafi a yayin da kasashen duniya ke fama da annobar. Ya ce, kasar Sin ta samar da rigakafi ga kasashe masu yawa musamman ma kasashe masu tasowa don ceton rayukan al’ummunsu, a yayin da kasashe masu sukuni a yammacin duniya suke kokarin tara allurai ba tare da raba wa kasashe masu tasowa ba, duk da cewa alluran sun ishe su kwarai da gaske.
Kwanan nan, kafar Bloomberg ta jera kasar Amurka a matsayi na farko a jerin kasashen da suka yi fice wajen yaki da annobar, abin da ya ba mu dariya sosai. Sai dai hakan ba zai taimaka ga gyara gaskiyar yadda Amurka ta ci tura a gida da ma waje wajen yaki da annobar. A hakika, wa ya zama na farko ba shi da muhimmanci, abin da ya fi muhimmanci shi ne a sauke nauyin da ke bisa wuya na samar da gudummawar yaki da annobar a duniya.
A yayin da kasashen duniya suke kara dunkulewa a waje guda, makomar ‘yan adam ma guda daya ce. A yayin da ake fuskantar annobar Covid-19, ba wanda zai iya samun kariya muddin dai kowa ya samu kariya. A ranar 16 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen Asiya da fasifik (APEC) ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa, kasarsa za ta samar da karin dala biliyan 3 a matsayin agaji na kasa da kasa cikin shekaru uku masu zuwa, don taimakawa aikin yaki da annobar COVID-19, da farfado da tattalin arziki da zamantakewa a kasashe masu tasowa, baya ga kuma ta samar da kudaden kafa karamin asusun hadin gwiwar APEC kan yaki da annobar COVID-19 da farfado da tattalin arziki, da nufin taimakawa tattalin arzikin kasashen kungiyar APEC farfadowa cikin sauri daga annoba.
Alkawari kaya ne. Kasancewarta kasar da ke sauke nauyin da ke wuyanta, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarin samar da rigakafi da ma sauran gudummawa, don hada kan kasa da kasa wajen tabbatar da kyakkyawar makomar ‘yan Adam, tare da kara ba da taimako ga shawo kan annobar da ma farfado da tattalin arzikin duniya.(Lubabatu Lei)