logo

HAUSA

Antonio Guterres ya bukaci sassan masu ruwa da tsaki a tashe tashen hankula da su yi amfani da gasar Tokyo wajen tsagaita wuta

2021-07-16 10:38:58 CRI

Antonio Guterres ya bukaci sassan masu ruwa da tsaki a tashe tashen hankula da su yi amfani da gasar Tokyo wajen tsagaita wuta_fororder_0716-Tokyo Olympics-Saminu

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki, a yankunan dake fuskantar tashe-tashen hankula, da su aiwatar da matakan tsagaida wuta, a lokacin gudanar gasar Olympic ta birnin Tokyo, wadda za a bude tun daga ranar 23 ga watan nan.

Mr. Guterres, ya ce cikin ’yan kwanaki masu zuwa, ’yan wasa daga sassan duniya daban daban za su isa kasar Japan, domin halartar gasar ta Olympic da ajin nakasassu na gasar. Ya ce ko shakka babu, wadannan ’yan wasa za su haye tarin wahalhalu kafin samun damar halartar gasar, wadda ke zuwa yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubalen annobar COVID-19.

Don haka ne Mr. Guterres ya ce, akwai bukatar nuna karfin hali da hadin kai, a yunkurin da duniya ke yi na wanzar da zaman lafiya a duniya. Ya ce akwai yarjejeniyar gasar Olympic, wadda ta tanadi dakatar da bude wuta yayin da gasar ke gudana, saboda haka al’ummun duniya da gwamnatocin kasashe, na iya amfani da tanadin ta, wajen tsagaida wuta, da kuma rungumar hanya mai dorewa ta wanzar da zaman lafiya.  (Saminu)