Amurka Za Ta Girbi Abin Da Ta Shuka Kan Batun Yankin Taiwan Na Kasar Sin
2021-07-16 19:34:31 CRI
By CRI Hausa
Jiya ne, wani jirgin saman sojan kasar Amurka ya sauka a yankin Taiwan na kasar Sin, wannan mataki ne na talaka kuma ya fusata kasar Sin, kana ya sabawa tanade-tanade dake cikin hadaddiyar sanarwa guda uku tsakanin kasashen biyu. Sin ta nuna rashin jin dadinta matuka tare da yin gargadi cewa, rundunar sojan ‘yantar da jama’ar kasar Sin, tana shirin kota-kwana, kuma za ta dauki matakin da ya dace a ko da yaushe don murkushe makarkashiya ko wani yunkuri kawo baraka tsakananin yankin Taiwan da babban yankin kasar.
Duniya ta kallai yadda, a ran 6 ga wata, Kurt Campbell babban jami’i mai kula da harkokin yankin Indiya-Pacific na hukumar tsaron fadar White House, lokacin da ya halarci taron tawagar Asiya ta kungiyar masana ta Amurka kwanan baya, inda ya nuna rashin goyon bayan samun ‘yancin yankin Taiwan, yana mai cewa, sun fahimci sarkakiyar lamarin. A wancan lokaci, galibin kafofin yada labarai na kasa da kasa sun yi imanin cewa, watakila gwamnatin Amurka na wannan karo, za ta fahimci irin manufofin yadda ya kamata da za ta dauka kan yankin Taiwan, amma kwanaki 10 kacal da suka gabata, jirgin sojan kasar Amurka ya sauka a wurin da nufin kulla alaka a fannin aikin soja.
Sin ba za ta tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe ba, kuma ba za ta yarda wata kasa ta tsoma mata baki a harkokin cikin gidanta ba. Ya kamata, a fahimci niyya da karfin jama’a da sojojin kasar Sin na kiyaye ikon mulki da cikakken yankin kasar.
Ba shakka, Sin za ta dunkule, ba wanda zai hana haka. (Amina Xu)